Fassarar Kur'ani

Mawallafi: Hafiz Muhammad Sa'id
Tarjarmar Kur'ani

Abin lura dangane da wannan littafin

Wanda ya tsara ya buga kuma ya yada

Muassasar Hasanain don yada al’adun Musulunci

Da fatan Allah Ta'ala ya datar da mu wajen kara gyara shi da fitar da shi bisa mafi kyawun sura

www.alhassanain.org/hausa

TARJAMAR KUR'ANI MAI DARAJA

Wallafar: Hafiz Muhammad Sa’id

hfazah@yahoo.com


Da Sunan Allah Ta'ala Mai Rahama Mai Jin Kai

KUR'ANI MADAUAKAKI:

"MU NE MUKA SAUKAR DA AMBATO KUMA MU MASU KARIYA NE GARESHI".

DAGA SURAR NABA'I ZUWA SURAR NASI


Surar Fatiha([1])

سورة الفاتحة

Ayoyinta 7 ne, Ana kiranta Uwar Littafi domin ta tara ilmin da yake a cikin Kur'ani a dunk'ule. Basmala a cikinta take ga k'ira'ar Asim, ruwayar Hafs, amma banda a k'ira'ar Warsh.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

1. Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai.

الْحَمْدُ لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ

2. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

اَلرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

3. Mai rahama mai jin k'ai.

مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ

4. Mai mallakar ranar sakamako.

إيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ

5. Kai kad'ai muke bautawa kuma kai kad'ai ne muke neman taimako.

اِهْدِنَا الصِّرَاطَ المُسْتَقِيمَ

6. Ka shiryar da mu tafarki madaidaici.

صِرَاطَ الَّذِينَ أَنعَمْتَ عَلَيهِمْ غَيرِ المَغضُوبِ عَلَيهِمْ وَلاَ الضَّالِّينَ

7. Tafarkin wad'anda ka yi wa ni'ima, ba wad'anda aka yi fushi da su ba, kuma ba b'atattu ba.

Ubangijin halittu ya tara ilmin Tafiyar da lamurran bayi da halitta su, kamar rayarwa, da matarwa, da ciyarwa, da shayarwa, da tufatarwa, Mai rahama Ya tara dukan rahamar duniya da dukkan ni'imomin samarwa gaba d'aya. Mai jin k'ai ya tara ni'imar duniya mai dogewa zuwa Lahira kamar ni'imar imani. Mai mallakar ranar sakamako, ya had'a dukan abin da ya shafi makoma. Kai muke bauta wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhidin bauta da ibada. Hanya madaidaiciya, ta had'a Littafin Allah da Ahlul Baiti (a.s) a matsayin wasiyyar Ma'aikin Allah. Wad'anda aka yi wa ni'ima, su ne Alayen Ibrahim da Alayen Muhammad (a.s). Wad'anda aka yi fushi da su, da kuma b'atattu, sun tara dukkan mutanen da suka kauce wa tafarki madaidaici.


Surar Labari([2])

سورة النبإ

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

عَمَّ يَتَسَاءَلُونَ

1. A kan me suke tambayar juna?

عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ

2. A kan muhimmin labari mai girma?

الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ

3. Wanda suke sab'a wa juna a cikinsa?

كَلَّا سَيَعْلَمُونَ

4. A'aha! Za su sani.

ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ

5. Kuma, a'aha! Za su sani.

أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا

6. Ashe, ba Mu sanya k'asa shimfida ba?

وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا

7. Da duwatsu turaku (ga rik'e k'asa)?

وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا

8. Kuma, Mun halitta ku maza da mata?

وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا

9. Kuma, Muka sanya barcinku hutawa?

وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا

10. Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا

11. Kuma, Muka sanya lokacin rana na neman abin rayuwa?

وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا

12. Kuma, Muka gina sammai bakwai masu k'arfi, , a samanku?

وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا

13. Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rana).

وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا

14. Kuma, Muka saukar ruwa mai yawan zuba daga cikakkun giragizai?

لِنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا

15. Domin, Mu fitar da k'waya da tsiri da shi?

وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا

16. Da itacen lambuna masu lillibniya?

إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا

17. Lalle ne, ranar rarrabewa ta kasance abin k'ayyade wa lokaci.

يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا

18. Ranar da za a yi busa a cikin k'aho, sai ku zo, jama'a-jama'a.

وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًا

19. Kuma, aka bud'e sama, sai ta kasance k'ofofi.

وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا

20. Kuma, aka tafiyar da duwatsu, sai suka kasance k'ura.

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا

21. Lalle ne, Jahannama ta kasance madakata.

لِلْطَّاغِينَ مَآبًا

22. Makoma ce ga masu k'etare iyakoki.

لَابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا

23. Suna, masu zama a cikinta, zamunna.

لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا

24. Ba su d'and'anar wani sanyi a cikinta, kuma ba su d'and'anar wani abin sha.

إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا

25. Sai dai tafasasshen ruwa da rub'ab'b'en jini.

جَزَاءً وِفَاقًا

26. Sakamako mai dacewa.

إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا

27. Lalle ne, su, sun kasance ba su fatar wani sauk'in hisabi.

وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا

28. Kuma, suka k'aryata da ayoyinMu, k'aryatawa!

وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا

29. Kuma kowane abu Mun k'ididdige shi, a rubuce.

فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا

30. Saboda haka ku d'and'ana, domin haka ba za Mu k'ara muku komai ba sai azaba.

إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا

31. Lalle ne, masu tak'awa na da wani wurin samun babban rabo.

حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا

32. Lambuna da inabobi.

وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا

33. Da cikakkun 'yan mata, tsaran juna.

وَكَأْسًا دِهَاقًا

34. Da hinjalan giya cikakku.

لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا

35. Ba sa jin yasassar magana a cikinta, kuma ba sa jin k'aryatawa.

جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًا

36. Sakamako daga Ubangijinka, kyauta mai yawa.

رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرحْمَنِ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا

37. Ubangijin sammai da k'asa da abin da yake a tsakaninsu, Mai rahama, ba su da ikon yin wata magana daga gare Shi.

يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرحْمَنُ وَقَالَ صَوَابًا

38. Ranar da Ruhi da mala'iku zasu tsaya a cikin sahu, ba sa magana, sai wanda Allah Ya yi masa izini, kuma ya fad'i abin da yake daidai.

ذَلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَى رَبِّهِ مَآبًا

39. Wancan shi ne yini na gaskiya, to wanda ya so, ya rik'i makoma zuwa ga Ubangijinsa.

إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا

40. Lalle ne, Mu, Mun yi muku gargad'in azaba makusanciya, ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayensa suka aikata, kuma kafiri ya ce; Kaicona, da dai na zama turb'aya!


Surar Masu Fizga([3])

سورة النازعات

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا

1. Ina rantsuwa da mala'iku masu fisgar rayuka da k'arfi.

وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا

2. Da masu d'aukar rayuka da sauk'i a cikin nishad'i.

وَالسَّابِحَاتِ سَبْحاً

3. Da masu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا

4. Sa'an nan, su zama masu gaugawa (da umurnin Allah) kamar suna tsere.

فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا

5. Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.

يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ

6. Ranar da mai girgiza abubuwa (busar farko) za ta kad'a.

تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ

7. Mai biyar ta (busa ta biyu) na biye.

قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ

8. Wasu zukata, a ranar nan, masu jin tsoro ne.

أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ

9. Alhali idanunsu na k'ask'antattu.

يَقُولُونَ أَئِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ

10. Suna cewa; Ashe lalle za a iya mayar da mu a kan sawunmu?

أَئِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً

11. Ashe, idan muka zama k'asusuwa rududdugaggu?

قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ

12. Suka ce; Waccan kam komawa ce, tab'ab'b'iya!

فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ

13. To, ita kam, tsawa guda kawai ce.

فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ

14. Sai kawai ga su a bayan k'asa.

هَلْ أتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى

15. Shin, labarin Musa ya zo maka?

إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى

16. A lokacin da Ubangijinsa Ya kiraye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato D'uwa?

اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَى

17. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi ya k'etare haddi.

فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَى أَن تَزَكَّى

18. Sai ka ce masa, Ko za ka so ka tsarkaka.

وَأَهْدِيَكَ إِلَى رَبِّكَ فَتَخْشَى

19. Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?

فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَى

20. Sai ya nuna masa ayar nan mafi girma.

فَكَذَّبَ وَعَصَى

21. Sai ya k'aryata, kuma ya sab'a.

ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَى

22. Sa'an nan ya juya baya, yana tafiya da sauri.

فَحَشَرَ فَنَادَى

23. Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَى

24. Sai ya ce; Ni ne Ubangijinku mafi d'aukaka.

فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَى

25. Saboda haka Allah Ya kama shi, domin azabar maganar k'arshe da ta farko.

إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَى

26. Lalle ne, a cikin wannan hak'ik'a akwai abin kula ga wanda yake tsoron Allah.

أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءَ بَنَاهَا

27. Shin, ku ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا

28. Ya d'aukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا

29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَلِكَ دَحَاهَا

30. Kuma, k'asa a bayan haka Ya mulmula ta.

أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا

31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyayarta.

وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا

32. Da duwatsu, Ya kafe su.

مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ

33. Domin jiyarwar dad'i a gare ku, kuma ga dabbobinku.

فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَى

34. To, idan uwar masifu mafi girma, ta zo.

يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَى

35. Ranar da mutum zai yi tunanin abin da ya aikata.

وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَى

36. Kuma, a bayyana Jahim ga mai gani.

فَأَمَّا مَن طَغَى

37. To, amma wanda ya yi girman kai.

وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا

38. Kuma, ya zab'i rayuwar duniya.

فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَى

39. To, hak'ik'a Jahim ita ce makoma.

وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى

40. Kuma, amma wanda ya ji tsoron tsayi a gaban Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى

41. To, lalle ne Aljanna ita ce makoma.

يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا

42. Suna tambayar ka game da alk'iyama, wai yaushe ne matabbatarta?

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا

43. Me ya had'a ka da ambatonta?

إِلَى رَبِّكَ مُنتَهَاهَا

44. Zuwa ga Ubangijinka k'arshen al'amarinta yake.

إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا

45. Kai mai gargad'i kawai ne ga mai tsoronta.

كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا

46. Kamar su a ranar da za su gan ta, ba su zauna ba face a lokacin marece ko hantsinta.


Surar Murtuke Fuska([4])

سورة عبس

Tana karantar da rashin bambanci tsakanin musulmi, rik'on addini da gaskiya shi ne d'aukaka, An ce wannan sura ta sauka ne lokaci da Abdullahi bn Maktum ya zo wajen Usman sai ya d'aure fuskarsa saboda yana makaho kuma mabuk'aci

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.

عَبَسَ وَتَوَلَّى

1. Ya had'a fuska kuma ya juya baya.

أَن جَاءَهُ الْأَعْمَى

2. Saboda makaho ya zo masa.

وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّى

3. To, me ya sanar da kai cewa watak'ila shi ne zai tsarkaka.

أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ الذِّكْرَى

4. Ko ya tuna, sai tunawar ta amfane shi?

أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى

5. Amma wanda ya wadatu da dukiya.

فَأَنتَ لَهُ تَصَدَّى

6. Sa'an nan kai kuma ka bijira zuwa gare shi!

وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّى

7. To, me zai cuce ka idan bai tsarkaka ba?

وَأَمَّا مَن جَاءَكَ يَسْعَى

8. Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugawa.

وَهُوَ يَخْشَى

9. Alhali shi yana jin tsoron Allah.

فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّى

10. Kai kuma ka shagala ga barinsa!

كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ

11. A'aha! Lalle ne, wannan tunatarwa ce.

فَمَن شَاء ذَكَرَهُ

12. Saboda wanda ya so ya tuna Shi.

فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ

13. A cikin littattafai ababan girmamawa.

مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍ

14. Ababan d'aukakawa, ababan tsarkakewa.

بِأَيْدِي سَفَرَةٍ

15. A hannayen mala'iku marubuta.

كِرَامٍ بَرَرَةٍ

16. Masu daraja, masu d'a'a ga Allah.

قُتِلَ الْإِنسَانُ مَا أَكْفَرَهُ

17. An la'ani mutum (kafiri), mamakin yawan kafircinsa!

مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ

18. Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ

19. Daga d'igon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya k'addara shi.

ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ

20. Sa'an nan Ya saukake masa hanyarsa.

ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ

21. Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنشَرَهُ

22. Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tayar da shi.

كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ

23. Hak'ik'a bai wada aikata abin da (Allah) Ya umurce shi ba.

فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ إِلَى طَعَامِهِ

24. To, mutum ya duba zuwa ga abincinsa.

أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا

25. Lalle ne Mu, Mun zubo ruwa, zubowa.

ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا

26. Sa'an nan, Muka tsattsage kasa tsattsagewa.

فَأَنبَتْنَا فِيهَا حَبًّا

27. Sa'an nan, Muka tsirar da k'waya ,a cikinta.

وَعِنَبًا وَقَضْبًا

28. Da inabi da ciyawa.

وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا

29. Da zaituni da itacen dabino.

وَحَدَائِقَ غُلْبًا

30. Da lambuna, masu yawan itace.

وَفَاكِهَةً وَأَبًّا

31. Da 'ya'yan itacen marmari, da makiyaya ta dabbobi.

مَّتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ

32. Domin jin dad'i a gareku, ku da dabbobinku.

فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ

33. To, idan mai tsawa (busa ta biyu) ta zo.

يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ

34. Ranar da mutum yake gudu daga dan'uwansa.

وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ

35. Da uwarsa da ubansa.

وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ

36. Da matarsa da d'iyansa.

لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ

37. Ga kowane mutum daga cikinsu, a ranar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ

38. Wasu fuskoki, a ranar nan, masu haske ne.

ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ

39. Masu dariya ne, masu bushara.

وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ

40. Wasu fuskoki, a ranar nan, akwai k'ura a kansu.

تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ

41. Bak'i zai rufe su.

أُوْلَئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ

42. Wad'annan su ne kafirai fajirai.


Surar Kisfewa([5])

سورة التكوير

Tana karantar da Tashin kiyama gaskiya ne, kuma Kur'ani gaskiya ne, daga Allah yake, babu ragi babu kari, ya taho ta hannun aminci daga Allah zuwa ga Annabi.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ

1. Idan aka kisfe rana.

وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ

2. Kuma idan taurari suka gurb'ace.

وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ

3. Kuma idan duwatsu aka tafiyar da su.

وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ

4. Kuma idan rak'uma masu cikkuna aka sake su wawai.

وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ

5. Kuma idan dabbobin daji aka tattara su.

وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ

6. Kuma idan tekuna aka mayar da su wuta.

وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ

7. Kuma idan rayuka aka aurar da su (ga matattu).

وَإِذَا الْمَوْؤُودَةُ سُئِلَتْ

8. Kuma idan wadda aka turbud'e ta da rai aka tambaye ta.

بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ

9. Saboda wane laifi ne aka kashe ta?

وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ

10. Kuma idan takardun ayyuka aka watsa su.

وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ

11. Kuma idan sama aka fed'e ta.

وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ

12. Kuma idan Jahim aka hura ta.

وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ

13. Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْ

14. Rai ya san abin da ya halartar.

فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ

15. To, ba sai Na yi rantsuwa da taurari matafa ba.

الْجَوَارِ الْكُنَّسِ

16. Masu gudu suna b'uya.

وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ

17. Da dare idan ya bayar da baya.

وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ

18. Da safiya idan ta yi lumfashi.

إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ

19. Lalle ne shi (Kur'ani), maganar wani manzo ne mai girma.

ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ

20. Mai k'arfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ

21. Wanda ake yi wa d'a'a ne, amintacce a can.

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ

22. Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ

23. Kuma lalle ne, ya gan shi a cikin sararin sama mabayyani.

وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ

24. Kuma shi, ga gaibi ba mai rowa ba ne.

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ

25. Kuma shi ba maganar shed'ni abin la'ana, ba ce.

فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ

26. Shin, to ina za ku tafi?

إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ

27. Lalle ne shi ba komai ba ne sai ambato ga talikai.

لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ

28. Ga wanda ya so daga cikinku, ya shiryu.

وَمَا تَشَاؤُونَ إِلَّا أَن يَشَاء اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ

29. Kuma ba zaku so ba sai idan Allah Ubangijin talikai ya yarda.

سورة الإنفطار

Surar Tsagewa ([6])

Tana karantar da gaskiyar Tashin Kiyama, kuma ayyukan mutum na duniya ana tsare da su domin hisabi da sakamako.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ

1. Idan sama ta tsage.

وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ

2. Kuma idan taurari suka watse.

وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ

3. Kuma idan tekuna aka facce su.

وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ

4. Kuma idan kaburbura aka tone su.

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ

5. Rai ya san abin da ya gabatar, da abin da ya jinkirtar.

يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ

6. Ya kai mutum! Me ya ruء e ka game da Ubangijinka, Mai karimci.

الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ

7. Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaita ka, Ya kuma tsakaita ka.

فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ

8. Ya gina ka a kan kowace irin sura Ya so.

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ

9. A'aha, ba haka ba, kuna k'aryatawa game da sakamako!ٍ

وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ

10. Lalle ne akwai matsara a kanku.

كِرَامًا كَاتِبِينَ

11. Masu daraja, marubuta.

يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ

12. Suna sanin abin da kuke aikatawa.

إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ

13. Lalle ne, masu d'a'a ga Allah suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ

14. Kuma lalle ne, fajirai, suna cikin Jahim.

يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ

15. Za su shige ta a ranar sakamako.

وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ

16. Ba za su faku daga gare ta ba.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ

17. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?

ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ

18. Sa'an nan, me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?

يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِلَّهِ

19. Rana ce da wani rai ba ya iya mallakar komai domin wani rai, al'amari a ranar nan ga Allah yake.


Surar Masu Tauye Awo([7])

سورة المطففين

Tana karantar da wajabcin tsare hak'k'ok'in mutane tsakaninsu a ciniki da wasu mu'amalolin zamantakewa.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ

1. Bone ya tabbata ga masu tauyewa.

الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُواْ عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ

2. Wadanda suke idan suka auna daga mutane suna cika mudu.

وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ

3. Kuma idan sun auna musu awon kwano ko awon sikeli, suna ragewa.

أَلَا يَظُنُّ أُولَئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ

4. Ashe! Wad'ancan ba sa tsammanin cewa tabbas ana tayar da su ba?

لِيَوْمٍ عَظِيمٍ

5. Domin yini mai girma.

يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ

6. Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta?

كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ

7. A'aha! Hak'ik'a littafin fajirai tabbas yana a cikin Sijjin.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ

8. Kuma, me ya sanar da kai abin da ake ce wa Sijjin?

كِتَابٌ مَّرْقُومٌ

9. Wani 1ittafi ne rubutacce.

وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ

10. Bone ya tabbata a ranar nan ga masu k'aryatawa.

الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ

11. Wad'anda suke k'aryatawa game da ranar sakamako.

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ

12. Babu mai k'aryatawa da ita sai dukkan mai k'etare haddi mai yawan zunubi.

إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ

13. Idan ana karanta masa ayoyinmu, sai ya ce: Tatsuniyoyin mutanen farko ne.

كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَى قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ

14. A'aha! Ba haka ba, abin da suka kasance suna aikatawa dai, ya yi tsatsa a cikin zukatansu.

كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ

15. A'aha! Hak'ik'a, su wad'anda ake shamakancewa daga Ubangijinsu ne a wannan ranar.

ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا الْجَحِيمِ

16. Sa'an nan, lalle ne, su masu shiga cikin Jahim ne.

ثُمَّ يُقَالُ هَذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ

17. Sannan a ce; Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna k'aryatawa da shi.

كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ

18. A'aha! Hak'ik'a littafin masu d'a'a yana a cikin Illiyyina?

وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ

19. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cewa Illiyyuna?

كِتَابٌ مَّرْقُومٌ

20. Wani littafi ne rubutacce.

يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ

21. Mukarrabai ne suke halartar sa.

إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ

22. Hak'ik'a masu d'a'a suna cikin ni'ima.

عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ

23. A kan karagu, suna ta kallo.

تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ

24. Kana sanin walwalin ni'ima a fuskokinsu.

يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ

25. Ana shayar da su daga wata giya wadda aka yunk'e a kan rufinta.

خِتَامُهُ مِسْكٌ وَفِي ذَلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ

26. K'arshen kurb'inta al'miski ne. To, a cikin wannan, masu rige su yi ta rige.

وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍ

27. Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnim yake.

عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ

28. Wani marmaro ne wanda muk'arrabai suke sha daga gare shi.

إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُواْ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ

29. Lalle ne, wad'anda suka kafirta sun kasance suna yi wa wad'anda suka yi imani dariya.

وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ

30. Kuma idan sun shud'e su sai su dinga yin zund'e.

وَإِذَا انقَلَبُواْ إِلَى أَهْلِهِمُ انقَلَبُواْ فَكِهِينَ

31. Kuma idan suka juya zuwa ga iyalansu, sai su tafi suna kakaci.

وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَؤُلَاءِ لَضَالُّونَ

32. Kuma idan sun gan su sai su ce; Lalle wad'annan b'atattu ne.

وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ

33. Alhali kuwa, ba a aike su ba domin su zama masu lura da su.

فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُواْ مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ

34. To, yau fa wad'anda suka yi imani, su ne suke yi wa kafirai dariya.

عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ

35. Suna masu kallo a kan karagu.

هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ

36. Shin an saka wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa?


Surar Kecewa([8])

سورة الإنشقاق

Tana karantar da tabbatar Tashin K'iyama, kuma duka abin da ake aikatawa idan ba na tattalin K'iyamar ba ne, to, ya zama wahalar da kai, maras amfani, da b'ata lokaci.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

إِذَا السَّمَاءُ انشَقَّتْ

1. Idan sama ta kece.

وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ

2. Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin sauraron.

وَإِذَا الْأَرْضُ مُدَّتْ

3. Kuma idan k'asa aka mike ta.

وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ

4. Kuma ta jefar da abin da yake a cikinta, ta wofinta daga kome.

وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ

5. Kuma ta saurari Ubangijinta, aka wajabta mata yin sauraren.

يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَى رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَاقِيهِ

6. Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahalar da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, kuma kai mai had'uwa da Shi ne.

فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِه

7. To, amma wanda aka bai wa littafinsa a damansa.

فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا

8. To, za a yi masa hisabi, hisabi mai sauk'i.

وَيَنقَلِبُ إِلَى أَهْلِهِ مَسْرُورًا

9. Kuma ya juya zuwa ga iyalinsa yana mai raha.

وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ وَرَاءَ ظَهْرِهِ

10. Kuma amma wanda aka bai wa littafinsa, daga wajen bayansa.

فَسَوْفَ يَدْعُو ثُبُورًا

11. To, zai dinga kiran halaka!

وَيَصْلَى سَعِيرًا

12. Kuma ya shiga sa'ir.

إِنَّهُ كَانَ فِي أَهْلِهِ مَسْرُورًا

13. Lal1e ne shi, ya kasance a cikin iyalinsa yana mai raha.

إِنَّهُ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ

14. Lalle ne ya yi zaton ba zai komo ba.

بَلَى إِنَّ رَبَّهُ كَانَ بِهِ بَصِيرًا

15. Na'am! Hak'ik'a Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.

فَلَا أُقْسِمُ بِالشَّفَقِ

16. To, ba sai Na rantse da shafak'i ba.

وَاللَّيْلِ وَمَا وَسَقَ

17. Da dare, da abin da ya k'unsa.

وَالْقَمَرِ إِذَا اتَّسَقَ

18. Da wata idan ya cika.

لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ

19. Lalle ne kuna hawan wani hali daga wani halin.

فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ

20. To, me ya same su, ba sa yin imani?

وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لَا يَسْجُدُونَ

21. Kuma idan an karanta Kur'ani garesu ba sa k'ask'an da kai?

بَلِ الَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ

22. Ba haka ba! wad'anda suka kafirta, sai k'aryatawa suke yi.

وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ

23. Alhali Allah Shi ne Mafi sani ga abin a suke tarawa.

فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

24. Saboda haka, ka yi musu bushara da azaba mai rad'ad'i.

إِلَّا الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ

25. Sai dai wad'anda suka yi imani, suka aikata ayyukan k'warai, suna da wani sakamako wanda ba ya yankewa.


Surar Taurari([9])

سورة البروج

Tana bayanin mugunyar ak'ibar masu wahalar da muminai a kan addininsu, ba da wata hujja ba ta shari'a

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الْبُرُوجِ

1. Ina rantsuwa da sama mai taurarin lissafin shekara.

وَالْيَوْمِ الْمَوْعُودِ

2. Da yinin da aka yi alk'awarin zuwansa.

وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ

3. Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta.

قُتِلَ أَصْحَابُ الْأُخْدُودِ

4. An la'ani mutanen rami.

النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ

5. Wuta ce wacce aka hura.

إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ

6. A lokacin da suke a gefenta a zazzaune.

وَهُمْ عَلَى مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ

7. Alhali su, bisa ga abin da suke aikatawa ga muminai, suna halarce.

وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلَّا أَن يُؤْمِنُوا بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ

8. Kuma ba su azabtar da su ba, sai kawai domin sun yi imani da Allah Mabuwayi, abin godewa.

الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ

9. Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da k'asa, kuma Allah a kan kome halarce Yake.

إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ الْحَرِيقِ

10. Lalle ne wad'anda suka fitini muminai maza da muminai mata, sa'an nan ba su tuba ba, to suna da azabar Jahannama, kuma suna da azabar gobara.

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ

11. Lalle ne wad'anda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan k'warai suna da gidajen Aljanna, k'oramu suna gudana daga k'ark'ashinsu, wancan abu fa shi ne rabo babba.

إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ

12. Hak'ik'a damk'ar Ubangijinka mai tsanani ce k'warai.

إِنَّهُ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ

13. Hak'ik'a shi ne Mai k'aga halitta, kuma Ya mayar da ita.

وَهُوَ الْغَفُورُ الْوَدُودُ

14. Kuma Shi ne Mai gafara, Mai bayyana soyayya.

ذُو الْعَرْشِ الْمَجِيدُ

15. Mai Al'arshi mai girma

فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ

16. Mai aikatawa ga abin da Yake nufi.

هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْجُنُودِ

17. Ko labarin rundanoni ya zo maka.

فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ

18. Fir'auna da samudawa?

بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي تَكْذِيبٍ

19. A'aha! wad'anda suka kafirta suna cikin k'aryatawa.

وَاللَّهُ مِن وَرَائِهِم مُّحِيطٌ

20. Alhali, Allah Mai kewaye daga bayansu ne.

بَلْ هُوَ قُرْآنٌ مَّجِيدٌ

21. A'aha! Shi Kur'ani ne mai girma.

فِي لَوْحٍ مَّحْفُوظٍ

22. A cikin Allo tsararre.

Ma'abota Rami: Ko kuma Mutanen Rami: Su ne mutanen Najiran da suka yi rami suka hura wuta a ciki, domin su k'one wanda ya yi imani da addinin Masih Isa domin su hana yad'uwarsa. Suka umurci kowane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo.


Surar Mai Aukowa([10])

سورة الطارق

Tana karantar da tsaron Al1ah ga kome bisa ga tsari, kuma kome asirinsa ne, sannan duk masu kaidi su sani cewa; Allah yana nan a madakata

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ

1. Ina rantsuwa da sama da mai aukowa da dare.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ

2. To, me ya sanar da kai abin da ake cewa mai aukowa da dare?

النَّجْمُ الثَّاقِبُ

3. Shi ne tauraron nan mai tsananin haske.

إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ

4. Babu wani rai face a kansa akwai wani mai tsaro.

فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ مِمَّ خُلِقَ

5. To, mutum ya duba, daga me aka halitta shi?

خُلِقَ مِن مَّاء دَافِقٍ

6. An halitta shi daga wani ruwa mai tunkud'ar juna.

يَخْرُجُ مِن بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ

7. Yana fita daga tsakanin tsatso da karankarman k'irji.

إِنَّهُ عَلَى رَجْعِهِ لَقَادِرٌ

8. Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyawa ne.

يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ

9. Ranar da ake jarrabawar asirai.

فَمَا لَهُ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ

10. Saboda haka, ba shi da wani karfi, kuma ba shi da wani mai taimako.

وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ

11. Ina rantsuwa da sama ma'abuciyar ruwa mai komawa yana yankewa.

وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ

12. Da k'asa ma'abuciyar tsagewa.

إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ

13. Hak'ik'a shi magana ce dalla-dalla (daki-daki).

وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ

14. Kuma shi ba bananci (kakaci da raha) ba ne.

إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا

15. Lalle ne su, suna k'ulla kaidi na sosai.

وَأَكِيدُ كَيْدًا

16. Kuma Ni, Ina (mayar da) kaidi sosai.

فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا

17. Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.


Surar Mafi D'aukaka([11])

سورة الأعلى

Tana karantar da cewa rayarwa da matarwa a hannun Allah suke, su kuma nau'i-nau'i ne

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى

1. Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi d'aukaka.

الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّى

2. Wanda Ya yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.

وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَى

3. Kuma Wanda Ya k'addara (abin da ya so) sannan Ya shiryar.

وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَى

4. Kuma Wanda Ya fitar da makiyaya.

فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَى

5. Sa'an nan Ya mayar da ita k'ek'asassa, bak'a.

سَنُقْرِؤُكَ فَلَا تَنسَى

6. Za mu karantar da kai, saboda haka ba za ka manta ba.

إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَى

7. Face abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake b'oye.

وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَى

8. Kuma za Mu sauk'ak'e maka zuwa ga mai sauk'i.

فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ الذِّكْرَى

9. Saboda baka, ka tunatar, idan tunatarwa za ta yi amfani.

سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَى

10. Wanda yake tsoron (Allah) Zai tuna.

وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى

11. Kuma shak'iyyi, zai nisanceta.

الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَى

12. Wanda zai shiga wuta mafi girma.

ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَى

13. Sa'an nan ba zai mutu ba a cikinta, kuma ba zai rayu ba.

قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّى

14. Lalle ne wanda ya tsarkaka ya samu babban rabo.

وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّى

15. Kuma ya ambaci sunan Ubangijinsa, sa'an nan ya yi salla.

بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا

16. Ba haka ba! Kuna dai zab'in rayuwar duniya ne.

وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَى

17. Alhalin Lahira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

إِنَّ هَذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَى

18. Hak'ik'a wannan yana cikin littattafan farko.

صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَى

19. Littattafan Ibrahim da Musa.


Surar Mai Rufewa([12])

سورة الغاشية

Tana karantar da yin hujja da abin da ake iya gani da ido domin a fahimci abin da ake gani da hankali, gwargwadon tunanin abokin magana.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ

1. Shin labarin (K'iyama) mai rufe (mutane da tsoronta) ya zo maka?

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ

2. Wasu fuskoki a ranar nan k'ask'antattu ne.

عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ

3. Masu aikin wahala ne, masu gajiya.

تَصْلَى نَارًا حَامِيَةً

4. Za su shiga wata wuta mai zafi.

تُسْقَى مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ

5. Ana shayar da su daga wani marmaro mai zafin ruwa.

لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ

6. Ba su da wani abinci face dai daga danyi.

لَا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِن جُوعٍ

7. Ba ya sanya k'iba, kuma ba ya wadatarwa daga yunwa.

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ

8. Wasu fuskoki a ranar nan masu ni'ima ne.

لِسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ

9. Masu yarda ne game da aikinsu.

فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ

10. A cikin Aljanna mad'aukakiya.

لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً

11. Ba za su ji yasassar magana ba, a cikinta.

فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ

12. A cikinta akwai marmaro mai gudana.

فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ

13. A cikinta akwai gadaje mad'aukaka.

وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ

14. Da kofuna ar'aje.

وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ

15. Da filoli (matasan kai) a jere.

وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ

16. Da katifu shimfid'e.

أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ

17. Ashe to ba zasu yi duba ga rakuma ba yadda aka halitta su?

وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ

18. Da zuwa ga sama yadda aka daukaka ta?

وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ

19. Da zuwa ga duwatsu yadda aka kafa su?

وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ

20. Da zuwa ga k'asa yadda aka shimfid'a ta?

فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنتَ مُذَكِّرٌ

21. Saboda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.

لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ

22. Kai ba mai tankwasawa a kansu ba ne.

إِلَّا مَن تَوَلَّى وَكَفَرَ

23. Sai dai duk wanda ya juya baya, kuma ya kafirta.

فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ

24. To, Allah zai yi masa azaba, azabar nan da take mafi girma.

إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ

25. Lalle ne, zuwa gare Mu komowarsu take.

ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُمْ

26. Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisabi.


Surar Alfijir([13])

سورة الفجر

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالْفَجْرِ

1. Ina rantsuwa da alfijiri.

وَلَيَالٍ عَشْرٍ

2. Da darare goma.

وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ

3. Da (adadi na) cika da (na) mara.

وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ

4. Da dare idan yana shud'ewa.

هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَمٌ لِّذِي حِجْرٍ

5. Ko a cikin wad'annan akwai abin rantsuwa ga mai hankali.

أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ

6. Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Adawa ba?

إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ

7. Iramawa masu sakon k'irar jiki.

الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلَادِ

8. Wad'anda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garuruwa.

وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ

9. Da samudawa wad'anda suka fasa duwatsu a cikin Wadi.

وَفِرْعَوْنَ ذِي الْأَوْتَادِ

10. Da Fir'auna mai turaku.

الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلَادِ

11. Wad'anda suka k'etare iyakarsu, a cikin garuruwa.

فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ

12. Sai suka yawaita yin b'arna a cikinsu.

فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ

13. Saboda haka Ubangijinka Ya zuba musu bulalar azaba.

إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ

14. Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

فَأَمَّا الْإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ

15. To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wato Ya girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce; Ubangijina Ya girmama ni.

وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ

16. Kuma idan Ya jarraba shi, wato Ya k'untata masa arzikinsa, sai ya ce; Ubangijina Ya wulak'anta ni.

كَلَّا بَل لَّا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ

17. A'aha! Bari wannan, ai ba kwa girmama maraya!

وَلَا تَحَاضُّونَ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ

18. Ba kwa kwad'aita wa junanku ga (tattalin) abincin matalauci!

وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا

19. Kuma kuna cin dukiyar gado, ci na tarawa.

وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا

20. Kuma kuna son dukiya, so mai yawa.

كَلَّا إِذَا دُكَّتِ الْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا

21. A'aha! Idan aka nik'e k'asa nik'ewa sosai.

وَجَاء رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا

22. Kuma Ubangijinka Ya zo, alhali mala'iku na jere, safu- safu.

وَجِيءَ يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ وَأَنَّى لَهُ الذِّكْرَى

23. Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunani. To, ina fa tunani yake a gare shi!

يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي

24. Yana dinga cewa, Kaicona, ina ma dai na gabatar (da aikin k'warai) domin rayuwata!

فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُ أَحَدٌ

25. To, a ranar nan babu wani mai yin azaba irin azabar Allah.

وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُ أَحَدٌ

26. Kuma babu wani mai d'auri irin d'aurinSa.

يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ

27. Ya kai rai mai natsuwa!

ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً

28. Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhali kana mai yarda, abin yardarwa.

فَادْخُلِي فِي عِبَادِي

29. Sabobda haka, ka shiga cikin .

وَادْخُلِي جَنَّتِي

30. Kuma ka shiga Aljannata.

Wadi: Shi ne "Wadil-kura" sunan wuri ne a k'asar Siriya "Sham".


Surar Gari([14])

سورة البلد

Tana karantar da cewa mutum an halitta shi cikin wahala, komai amfaninsa idan ya bi umurnin Allah ko kuma cutarsa idan ya sab'a wa umurnin Allah

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

لَا أُقْسِمُ بِهَذَا الْبَلَدِ

1. Ba sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.

وَأَنتَ حِلٌّ بِهَذَا الْبَلَدِ

2. Da kuma kai kana mai sauka a cikin wannan gari.

وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ

3. Da mahaifi da abin da ya haifa.

لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي كَبَدٍ

4. Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.

أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ

5. Shin ko yana zaton babu wani mai iya samun iko a kansa?

يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا

6. Yana cewa; Na kashe dukiya mai yawa.

أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُ أَحَدٌ

7. Shin, ko yana zaton cewa wani bai gan shi ba?

أَلَمْ نَجْعَل لَّهُ عَيْنَيْنِ

8. Shin, ba Mu sanya masa idanu biyu ba?

وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ

9. Da harshe, da leb'b'a biyu.

وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ

10. Kuma muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu?

فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ

11. To, don mene ne bai shiga Ak'aba ba?

وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ

12. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake ce wa Ak'aba?

فَكُّ رَقَبَةٍ

13. Ita ce fansar wuyan bawa.

أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ

14. Ko kuma ciyar da ma'abucin yunwa, a cikin yini.

يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ

15. Ga maraya ma'abucin zumunta.

أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ

16. Ko kuwa wani matalauci ma'abucin turb'aya.

ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ

17. Sa'an nan kuma ya kasance daga wad'anda suka yi imani, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hak'uri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi.

أُوْلَئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ

18. Wad'annan ne ma'abuta albarka.

وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ

19. Kuma wad'anda suka kafirta da ayoyinmu, su ne ma'abuta shu'umci.

عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌ

20. A kansu akwai wata wuta abar kullewa.


Surar Rana([15])

سورة الشمس

Tana karantar da cewa idan azaba ta sauka a kan mutane takan shafi mai laifi da wanda ba shi da laifi daga cikinsu, da kuma nuni zuwa ga had'arin k'aryata ayar Allah mad'aukaki.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai.

وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَا

1. Ina rantsuwa da rana da hantsinta.

وَالْقَمَرِ إِذَا تَلَاهَا

2. Kuma da wata idan ya bi ta.

وَالنَّهَارِ إِذَا جَلَّاهَا

3. Da yini a lokacin da ya bayyana ta.

وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَاهَا

4. Da dare a lokacin da ya ke rufe ta.

وَالسَّمَاءِ وَمَا بَنَاهَا

5. Da sama da abin da ya gina ta.

وَالْأَرْضِ وَمَا طَحَاهَا

6. Da k'asa da abin da ya shimfid'a ta.

وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَا

7. Da rai da abin da ya daidaita shi.

فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَا

8. Sa'an nan ya sanar da shi fajircinsa da shiryuwarsa.

قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَا

9. Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sami babban rabo.

وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّاهَا

10. Kuma lalle ne wanda ya turbud'e shi (da laifi) ya tab'e.

كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَاهَا

11. Samudawa sun k'aryata domin girman kansu.

إِذِ انبَعَثَ أَشْقَاهَا

12. A lokacin da mafi shak'awarsu ya tafi.

فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ نَاقَةَ اللَّهِ وَسُقْيَاهَا

13. Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsoratar da ku ga rakumar Allah da ruwan shanta!"

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنبِهِمْ فَسَوَّاهَا

14. Sai suka k'aryata shi, sa'an nan suka soke ta. Saboda haka Ubangijinsu Ya darkake su saboda zunubinsu kuma ya daidaita ta (azabar).

وَلَا يَخَافُ عُقْبَاهَا

15. Kuma ba ya tsoron ak'ibarta (ita halakawar).


Surar Dare([16])

سورة الليل

Tana karantar da dangantaka tsakanin d'abi'a da halitta da aK'ibar mutum bisa aikinsa, da kuma kasuwar abubuwa tsakanin alheri da sharri.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَى

1. Ina rantsuwa da dare a lokacin da yake rufewa.

وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّى

2. Da lokacin rana yayin da bayyana.

وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَى

3. Da abin da ya halitta namiji da mace.

إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّى

4. HaK'iK'a ayyukanku, mabambanta ne.

فَأَمَّا مَن أَعْطَى وَاتَّقَى

5. To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taK'awa.

وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَى

6. Kuma ya gaskata kalma mai kyawo.

فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَى

7. To, za Mu sauK'aK'e masa har ya kai ga sauki.

وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَى

8. Kuma amma wanda ya yi rowa, kuma ya wadatu da kansa.

وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَى

9. Kuma ya K'aryatar da kalma mai kyawo.

فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَى

10. To, za Mu sauK'aK'e masa har ya kai ga tsanani.

وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّى

11. Kuma dukiyarsa ba ta wadatar masa da komai idan ya gangara (wuta).

إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَى

12. Lalle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.

وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَى

13. Kuma lalle ne Lahira da duniya Namu ne.

فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّى

14. Saboda haka, Na yi maku gargad'i da wuta mai babbaka.

لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى

15. Babu mai shigarta sai mafi shaK'awa.

الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّى

16. Wanda ya K'aryata, kuma ya juya baya.

وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى

17. Kuma mafi taK'awa zai nisance ta.

الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّى

18. Wanda yake bayar da dukiyarsa ,alhali yana tsarkaka.

وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَى

19. Alhali babu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake neman sakamakonta.

إِلَّا ابْتِغَاء وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَى

20. Face dai neman yardar Ubangijinsa Mafi d'aukaka.

وَلَسَوْفَ يَرْضَى

21. Kuma tabbas da sannu zai yarda.


Surar Hantsi([17])

سورة الضحى

Tana karantar da ni'imomin da Allah Ya yi wa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da neman ya yi godiya a kansu ta hanyar biyayya ga umarnin Allah.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالضُّحَى

1. Ina rantsuwa da hantsi

وَاللَّيْلِ إِذَا سَجَى

2. Da dare a lokacin da ya rufe (da duhunsa)

مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَى

3. Ubangijinka bai K'yale ka ba, kuma bai K'i kaba

وَلَلْآخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ الْأُولَى

4. Kuma lalle K'arshe ce mafi alheri a gare ka daga farko

وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَى

5. Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta ba ka kyauta sai ka yarda.

أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَآوَى

6. Ashe, bai same ka maraya ba, sa'an nan Ya yi maka mafaka?

وَوَجَدَكَ ضَالًّا فَهَدَى

7. Kuma Ya same ka ba ka da shari'a, sai Ya shiryar da kai?

وَوَجَدَكَ عَائِلًا فَأَغْنَى

8. Kuma Ya same ka matalauci, sai Ya wadata ka?

فَأَمَّا الْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ

9. Saboda haka, amma maraya, to, kada ka rinjaye shi.

وَأَمَّا السَّائِلَ فَلَا تَنْهَرْ

10. Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa kyara.

وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ

11. Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka fad'a.


Surar Yalwatawa([18])

سورة الشرح

Tana nuna ni'imomin da Allah Ya yi wa Annabi, (s.a.w) domin ya K'ara godiya ga Allah (s.w.t)

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ

1. Shin ba Mu yalwata maka zuciyarka ba.

وَوَضَعْنَا عَنكَ وِزْرَكَ

2. Kuma Muka saryar maka da nauyinka.

الَّذِي أَنْقَضَ ظَهْرَكَ

3. Wanda ya nauyaya bayanka.

وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ

4. Kuma Muka d'aukaka maka ambatonka.

فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا

5. To, lalle ne tare da tsanani akwai wani sauK'i.

إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا

6. Lalle ne tare da tsanani akwai wani sauK'in.

فَإِذَا فَرَغْتَ فَانصَبْ

7. Saboda haka idan ka K'are sai ka kafu.

وَإِلَى رَبِّكَ فَارْغَبْ

8. Kuma ka yi kwad'ayi zuwa ga Ubangijinka.


Surar B'aure([19])

سورة التين

Tana karantar da cewa dukkan abin da ya shafi imani da aiki na gari ba ya tab'ewa, amma sauran abubuwa suna halaka

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

وَالتِّينِ وَالزَّيْتُونِ

Ina rantsuwa da B'aure da Zaitun.

وَطُورِ سِينِينَ

Da Dutsen Sina.

وَهَذَا الْبَلَدِ الْأَمِينِ

Da wannan gari amintacce.

لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ

Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon daidaito.

ثُمَّ رَدَدْنَاهُ أَسْفَلَ سَافِلِينَ

Sannan Muka mayar da shi mafi K'asK'antar K'asK'antattu.

إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ

Sai dai wad'anda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka na K'warai, To wadannan suna da sakamako wanda ba ya yankewa.

فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِالدِّينِ

To, bayan haka me ya sanya ka K'aryata sakamako.

أَلَيْسَ اللَّهُ بِأَحْكَمِ الْحَاكِمِينَ

Ashe Allah ba Shi ne Mafi iya hukuncin masu hukunci ba?


Surar Gudan Jini([20])

سورة العلق

Tana karantar da cewa karatu shi ne gaba da komai, amma a gama shi da sunan Allah, kuma duk wanda ya kauce wa hanyar Allah zai samu uK'uba

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ

1. Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

خَلَقَ الْإِنسَانَ مِنْ عَلَقٍ

2. Ya hahitta mutum daga gudan jini.

اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ

3. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.

الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ

4. Shi ne wannan da ya koyar da alK'alami.

عَلَّمَ الْإِنسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ

5. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

كَلَّا إِنَّ الْإِنسَانَ لَيَطْغَى

6. A'aha! Lalle, ne mutum yana girman kai.

أَن رَّآهُ اسْتَغْنَى

7. Domin ya ga kansa, ya wadatu.

إِنَّ إِلَى رَبِّكَ الرُّجْعَى

8. HaK'iK'a zuwa ga Ubangijinka makoma take.

أَرَأَيْتَ الَّذِي يَنْهَى

9. Shin, ka ga wanda ke hana.

عَبْدًا إِذَا صَلَّى

10. Bawa idan ya yi salla?

أَرَأَيْتَ إِن كَانَ عَلَى الْهُدَى

11. Ashe, ka gani, idan ya kasance a kan shiriya?

أَوْ أَمَرَ بِالتَّقْوَى

12. Ko ya yi umurni da taK'awa?

أَرَأَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّى

13. Ashe, ka gani, idan ya K'aryata, kuma ya juya baya?

أَلَمْ يَعْلَمْ بِأَنَّ اللَّهَ يَرَى

14. Ashe, bai sani ba cewa Allah Yana gani?

كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًا بِالنَّاصِيَةِ

15. A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, tabbas zamu ja gashin maK'warK'wad'a.

نَاصِيَةٍ كَاذِبَةٍ خَاطِئَةٍ

16. MaK'warK'wad'a, maK'aryaciya, mai laifi.

فليدع نادية

17. To sai ya kira K'ungiyarsa.

سَنَدْعُ الزَّبَانِيَةَ

18. Zamu kira zabaniyawa.

كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِبْ

19. A'aha kada ka bi shi, kuma ka yi sujada, ka nemi kusanci.


Surar Daraja([21])

سورة القدر

Tana karantar da son Allah ga wannan al'umma ta Musulmi da Ya ba su Dare mai Daraja "Lailatul K'adr" domin Ya yawaita ladar ayyukansu ko da yake rayukansu ba su da tsawo kamar na al'ummomin farko, kamar yadda take nuna cewa; alaK'ar Allah (s.w.t) da bayinsa ba ta yankewa da yankewar Annabci.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai.

إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ

1. Lalle ne Mu, Mun saukar da shi a cikin Dare mai daraja.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا لَيْلَةُ الْقَدْرِ

2. To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul K'adari?

لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍ

3. Lailatul K'adari mafi alheri ne daga watanni dubu.

تَنَزَّلُ الْمَلَائِكَةُ وَالرُّوحُ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِم مِّن كُلِّ أَمْرٍ

4. Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu daga kowane umurni.

سَلَامٌ هِيَ حَتَّى مَطْلَعِ الْفَجْرِ

5? Aminci ne shi har b'ollowar alfijiri.


Surar Hujja([22])

سورة البينة

Tana karantar da halayen kifirai da mutanen Littafi, wato Yahudu da Nasara game da Annabi (s.a.w), da Mushirikai tun gabanin da kuma bayan bayyanarsa.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin K'ai

لَمْ يَكُنِ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّى تَأْتِيَهُمُ الْبَيِّنَةُ

1. Wad'anda suka kafirta daga mutanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har sai da hujja ta zo musu.

رَسُولٌ مِّنَ اللَّهِ يَتْلُو صُحُفًا مُّطَهَّرَةً

2. Wani Manzo daga Allah yana karanta wasu takardu masu tsarki.

فِيهَا كُتُبٌ قَيِّمَةٌ

3. A cikinsu akwai wasu littattafai masu d'aukaka.

وَمَا تَفَرَّقَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءتْهُمُ الْبَيِّنَةُ

4. Kuma wad'anda aka bai wa Littafi ba su rarrabu ba sai bayan hujja ta zo musu.

وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاء وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ

5. Kuma ba a umarce su da komai ba sai su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini gare Shi, masu daidaito, kuma su tsayar da salla, kuma su bayar da zakka, kuma wannan shi ne addinin nagarta.

إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُوْلَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ

6. HaK'iK'a ne wad'anda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai suna cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta, wad'annan su ne mafi sharrin talikai.

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُوْلَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ

7. HaK'iK'a wad'annan nan da suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari, wad'annan su ne mafifitan talikai.

جَزَاؤُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَّضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُ

8. Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar Adnu, K'oramu suna gudana daga K'arK'ashinsu suna madawwama a cikinta har abada, Allah Ya yarda da su, kuma su ma sun yarda da Shi, wannan (sakamako ne) ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa.


Surar Girgiza([23])

سورة الزلزلة

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا

1. Idan aka girgiza k'asa girgizawarta.

وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا

2. Kuma k'asa ta fitar da kayan nauyin da suke cikinta.

وَقَالَ الْإِنسَانُ مَا لَهَا

3. Kuma mutum ya ce: Mene ne ya same ta?.

يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا

4. A ranar nan zata fad'i labaranta.

بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَى لَهَا

5. Cewa Ubangijinka ne ya yi mata umarni.

يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتاً لِّيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ

6. A ranar nan mutane zasu zo jama'a-jama'a domin a nuna musu ayyukansu.

فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْراً يَرَهُ

7. To wanda ya aikta wani aiki gwargwadon nauyin zarra na alheri, zai gan shi.

وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرّاً يَرَهُ

8. Kuma wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.


Surar Dawakai([24])

سورة العاديات

بسم الله الرحمن الرحيم

Allah Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحاً

1. Ina rantsuwa da dawakai masu gudu, suna masu k'ugin ciki.

فَالْمُورِيَاتِ قَدْحاً

2. Da masu k'yasta wuta k'yastawa.

فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحاً

3. Sannan da masu kai hari lokacin Asuba.

فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعاً

4. Sai su tayar da k'ura da shi (harin).

فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعاً

5. Sai su kutsa cikin jama'ar mayak'a da ita (k'urar).

إِنَّ الْإِنسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ

6. Hak'ik'a mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

وَإِنَّهُ عَلَى ذَلِكَ لَشَهِيدٌ

7. Kuma lalle shi mai sheda ne a kan hakan.

وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ

8. Kuma lalle shi mai tsananin so ne ga alheri.

أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ ‏

9. Shin ba ya sanin idan aka tone abin da yake cikin kaburbura.

وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ

10. Kuma aka bayyana abin da yake cikin zukata.

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌ

11. Lalle Ubangijinsu masani ne game da su a wannan ranar.


Surar Mai K'wank'wasa([25])

سورة القارعة

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

الْقَارِعَةُ

1. Mai K'wank'wasa.

مَا الْقَارِعَةُ

2. Mece ce mai k'wank'wasa.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ

3. Kuma me ya sanar da kai mece ce mai k'wank'wasa.

يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ

4. Ranar da mutane zasu kasance kamar fari masu watsuwa.

وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنفُوشِ

5. Kuma duwatus su kasance kamar gashin suf da aka sab'e.

فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ

6. To amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ

7. To shi yana cikin wata rayuwa yardajjiya.

وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ

8. To amma kuma wanda ma'aunansa suka yi sako-sako.

فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ

9. To uwarsa Hawiya ce.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ

10. Me ya sanar da kai mece ce ita?.

نَارٌ حَامِيَةٌ

11. Wata wuta ce mai zafi.


Surar Yawan Tara Arziki([26])

سورة التكاثر

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

أَلْهَاكُمُ التَّكَاثُرُ

1. Rigen Yawan tara arziki ne ya shagaltar da ku.

حَتَّى زُرْتُمُ الْمَقَابِرَ

2. Har kuka ziyarci kaburbura.

كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ

3. A'aha! Zaku sani.

ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ

4. Sannan tabbas zaku sani.

كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ الْيَقِينِ

5. Hak'ik'a da ku san sani na yak'ini.

لَتَرَوُنَّ الْجَحِيمَ

6. Da kun ga wutar Jahim.

ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ الْيَقِينِ

7. Kuma tabbas zaku gan ta idanu k'uru-k'uru.

ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ

8. Sannan tabbas za a tambaye ku a wannan ranar game da ni'imar.


Surar Zamani([27])

سورة العصر

بسم الله الرحمن الرحيم

Allah Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

وَالْعَصْرِ

1. Ina rantsuwa da zamani

إِنَّ الْإِنسَانَ لَفِي خُسْرٍ

2. Hak'ik'a mutum yana cikin hasara.

إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ

3. Sai dai wad'anda suka yi imani, kuma suka yi ayyukan k'warai, kuma suka yi wa juna wasici da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasici da yin hak'uri.


Surar Mai Zumde([28])

سورة الهُمَزَة

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

وَيْلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ

1. Azaba ta tabbata ga dukkan wani, mai zumd'e, mai gatsine.

الَّذِي جَمَعَ مَالاً وَعَدَّدَهُ

2. Wanda ya tara dukiya ya yi tattalinta.

يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُ أَخْلَدَهُ

3. Yana tsammanin dukiyarsa zata dawwamar da shi.

كَلَّا لَيُنبَذَنَّ فِي الْحُطَمَةِ

4. A'aha! Lalle sai an jefa shi a cikin hud'ama.

وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحُطَمَةُ

5. Kuma me ya sanar da kai ko mece ce hud'ama.

نَارُ اللَّهِ الْمُوقَدَةُ

6. Wutar Allah ce abar hurawa.

الَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى الْأَفْئِدَةِ

7. Wacce take lek'awa a kan zuciya.

إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌ

8. Hak'ik'a ita abar kullewa ce a kansu.

فِي عَمَدٍ مُّمَدَّدَةٍ

9. A cikin wasu ginshik'ai mik'ak'k'u.


Surar Giwa([29])

سورة الفيل

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصْحَابِ الْفِيلِ

1. Ashe ba ka ga yadda ubangijinka ya aikata ga mutanen giwa ba?

أَلَمْ يَجْعَلْ كَيْدَهُمْ فِي تَضْلِيلٍ

2. Ashe bai sanya kaidinsu a cikin tab'ewa ba.

وَأَرْسَلَ عَلَيْهِمْ طَيْراً أَبَابِيلَ

3. Kuma ya aika musu da wasu tsuntsaye gungu-gungu.

تَرْمِيهِم بِحِجَارَةٍ مِّن سِجِّيلٍ

4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumb'un wuta.

فَجَعَلَهُمْ كَعَصْفٍ مَّأْكُولٍ

5. Sai ya sanya su kamar karmami abin cinyewa.

سورة قريش

Surar K'uraishawa([30])

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

لِإِيلَافِ قُرَيْشٍ

1. Saboda sabon k'uraishawa.

إِيلَافِهِمْ رِحْلَةَ الشِّتَاء وَالصَّيْفِ

2. Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara.

فَلْيَعْبُدُوا رَبَّ هَذَا الْبَيْتِ

3. Don haka sai su bauta wa ubangijin wannan d'akin.

الَّذِي أَطْعَمَهُم مِّن جُوعٍ وَآمَنَهُم مِّنْ خَوْفٍ

4. Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga wani tsoro.


Surar taimako([31])

سورة الماعون

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

أَرَأَيْتَ الَّذِي يُكَذِّبُ بِالدِّينِ

1. Shin ka ga wanda yake k'aryatawa game da sakamako?

فَذَلِكَ الَّذِي يَدُعُّ الْيَتِيمَ

2. To wannan shi ne yake tunkud'e maraya.

وَلَا يَحُضُّ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ

3. Kuma ba ya kwad'aitarwa bisa ciyarwar miskini.

فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ

4. To azaba ta tabbata ga masallata.

الَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ

5. Wad'annan da suke masu shagala daga sallarsu.

الَّذِينَ هُمْ يُرَاؤُونَ

6. Wad'annan da suke yin riya.

وَيَمْنَعُونَ الْمَاعُونَ

7. Kuma suke hana taimako.


Surar Alheri Mai Yawa([32])

سورة الكوثر

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ

1. Lalle ne mu, mun yi maka alheri mai yawa.

فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ

2. Saboda haka ka yi salla domin ubangijinka, kuma ka yi suka (soke taguwa/rak'umi).

إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ

3. Hak'ik'a mai aibata ka shi ne mai yankakken baya (maras albarka).


Surar Kafirai([33])

سورة الكافرون

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

قُلْ يَا أَيُّهَا الْكَافِرُونَ

1. Ka ce; Ya ku kafirai.

لَا أَعْبُدُ مَا تَعْبُدُونَ

2. Ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba.

وَلَا أَنتُمْ عَابِدُونَ مَا أَعْبُدُ

3. Kuma ba zaku zama masu bauta ga abin da nake bauta wa ba.

وَلَا أَنَا عَابِدٌ مَّا عَبَدتُّمْ

4. Kuma ni ba zan zama mai bauta wa abin da kuke bauta wa ba.

وَلَا أَنتُمْ عَابِدُونَ مَا أَعْبُدُ

5. Kuma ku ba zaku zama masu bauta wa abin da nake bauta wa ba.

لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ

6. Addininku na gareku, kuma addinina yana gareni.


Surar Cin Nasara([34])

سورة النصر

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai

إِذَا جَاء نَصْرُ اللَّهِ وَالْفَتْحُ

1. Idan taimakon Allah da cin nasara suka zo.

وَرَأَيْتَ النَّاسَ يَدْخُلُونَ فِي دِينِ اللَّهِ أَفْوَاجاً

2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah jama'a-jama'a.

فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَاسْتَغْفِرْهُ إِنَّهُ كَانَ تَوَّاباً

3. To, ka yi tasbihi da gode wa ubangijinka, kuma ka neme shi gafararsa, Lalle shi ya kasance mai yawan karb'ar tuba ne.


Surar Harshen wuta([35])

سورة اللهب

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

تَبَّتْ يَدَا أَبِي لَهَبٍ وَتَبَّ

1. Hannaye biyu na AbuLahab sun halaka, kuma ya halaka.

مَا أَغْنَى عَنْهُ مَالُهُ وَمَا كَسَبَ

2. Dukiyarsa da abin da ya tara, ba su tsare masa komai ba.

سَيَصْلَى نَاراً ذَاتَ لَهَبٍ

3. Zai shiga wuta mai huruwa.

وَامْرَأَتُهُ حَمَّالَةَ الْحَطَبِ

4. Tare da matarsa mai d'aukar itace.

فِي جِيدِهَا حَبْلٌ مِّن مَّسَدٍ

5. A cikin wuyanta akwai igiyar kaba.


Surar Tsarkakewa([36])

سورة الإخلاص

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ

1. Ka ce: Shi ne Allah makad'aici.

اللَّهُ الصَّمَدُ

2. Allah Sid'if yake.

لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ

3. Bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba.

وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُواً أَحَدٌ

4. Kuma babu wani da ya kasance tamka a gareshi.


Surar Asuba([37])

سورة الفلق

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ

1. Ka ce ina neman tsari ga ubangijin safiya.

مِن شَرِّ مَا خَلَقَ

2. Daga sharrin abin da ya halitta.

وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ

3. Daga sharirn dare idan ya yi duhu.

وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ

4. Daga sharrin mata masu tofi a cikin k'ulle-k'ulle.

وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ

5. Daga sharrin mahassadi yayin da ya yi hassada.


Surar Mutane([38])

سورة الناس

بسم الله الرحمن الرحيم

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin k'ai

قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ

1. Ka ce ina neman tsari ga ubangijin mutane.

مَلِكِ النَّاسِ

2. Mamallakin mutane.

إِلَهِ النَّاسِ

3. Abin bautar mutane.

مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ

4. Daga sharrin mai waswasi mai b'oyewa.

الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ

5. Wanda yake sanya waswasi a cikin zukatan mutane.

مِنَ الْجِنَّةِ وَ النَّاسِ

6. Daga aljanu da mutane.



Makomar Bincike

_____________________

([1]) Surar Fatiha, Al-kur’ani mai girma, sura ta 01

([2]) Surar Naba’i, Al-kur’ani mai girma, sura ta 78

([3]) Surar Nazi’ati, Al-kur’ani mai girma, sura ta 79

([4]) Surar Abasa, Al-kur’ani mai girma, sura ta 80

([5]) Surar Takwiri, Al-kur’ani mai girma, sura ta 81

([6]) Surar Infidari, Al-kur’ani mai girma, sura ta 82

([7]) Surar Mudaffifin, Al-kur’ani mai girma, sura ta 83

([8]) Surar Inshikaki, Al-kur’ani mai girma, sura ta 84

([9]) Surar Buruj, Al-kur’ani mai girma, sura ta 85

([10]) Surar Dariki Al-kur’ani mai girma, sura ta 86

([11]) Surar A’ala Al-kur’ani mai girma, sura ta 87

([12]) Surar Gashiyah, Al-kur’ani mai girma, sura ta 88

([13]) Surar Fajri, Al-kur’ani mai girma, sura ta 89

([14]) Surar Baladi, Al-kur’ani mai girma, sura ta 90

([15]) Surar Shamsi, Al-kur’ani mai girma, sura ta 91

([16]) Surar Laili, Al-kur’ani mai girma, sura ta 92

([17]) Surar Dhuha, Al-kur’ani mai girma, sura ta 93

([18]) Surar Sharhi, Al-kur’ani mai girma, sura ta 94

([19]) Surar Tini, Al-kur’ani mai girma, sura ta 95

([20]) Surar Alaki, Al-kur’ani mai girma, sura ta 96

([21]) Surar Kadari, Al-kur’ani mai girma, sura ta 97

([22]) Surar Bayyina, Al-kur’ani mai girma, sura ta 98

([23]) Surar Zilzali, Al-kur’ani mai girma, sura ta 99

([24]) Surar Aadiyati, Al-kur’ani mai girma, sura ta 100

([25]) Surar Kari’ah, Al-kur’ani mai girma, sura ta 101

([26]) Surar Takasuri Al-kur’ani mai girma, sura ta 102

([27]) Surar Asri Al-kur’ani mai girma, sura ta 103

([28]) Surar Humazah, Al-kur’ani mai girma, sura ta 104

([29]) Surar Fili Al-kur’ani mai girma, sura ta 105

([30]) Surar Kuraishu, Al-kur’ani mai girma, sura ta 106

([31]) Surar Maa’un, Al-kur’ani mai girma, sura ta 107

([32]) Surar Kausar, Al-kur’ani mai girma, sura ta 108

([33]) Surar Kafirun, Al-kur’ani mai girma, sura ta 109

([34]) Surar Nasri, Al-kur’ani mai girma, sura ta 110

([35]) Surar Masadi, Al-kur’ani mai girma, sura ta 111

([36]) Surar Ikhlas, Al-kur’ani mai girma, sura ta 112

([37]) Surar Falaki, Al-kur’ani mai girma, sura ta 113

([38]) Surar Nasi, Al-kur’ani mai girma, sura ta 114


Abin Da Littafin Ya Kunsa

TARJAMAR KUR'ANI MAI DARAJA 1

Wallafar: Hafiz Muhammad Sa’id 1

Surar Fatiha([1]) 3

Surar Labari([2]) 4

Surar Masu Fizga([3]) 7

Surar Murtuke Fuska([4]) 10

Surar Kisfewa([5]) 13

Surar Tsagewa 14

Surar Masu Tauye Awo([7]) 16

Surar Kecewa([8]) 19

Surar Taurari([9]) 21

Surar Mai Aukowa([10]) 23

Surar Mafi D'aukaka([11]) 25

Surar Mai Rufewa([12]) 27

Surar Alfijir([13]) 29

Surar Gari([14]) 31

Surar Rana([15]) 33

Surar Dare([16]) 35

Surar Hantsi([17]) 37

Surar Yalwatawa([18]) 38

Surar B'aure([19]) 39

Surar Gudan Jini([20]) 40

Surar Daraja([21]) 42

Surar Hujja([22]) 43

Surar Girgiza([23]) 44

Surar Dawakai([24]) 45

Surar Mai K'wank'wasa([25]) 46

Surar Yawan Tara Arziki([26]) 47

Surar Zamani([27]) 48

Surar Mai Zumde([28]) 49

Surar Giwa([29]) 50

Surar taimako([31]) 51

Surar Alheri Mai Yawa([32]) 52

Surar Kafirai([33]) 53

Surar Cin Nasara([34]) 54

Surar Harshen wuta([35]) 55

Surar Tsarkakewa([36]) 56

Surar Asuba([37]) 57

Surar Mutane([38]) 58

Makomar Bincike 60

Abin Da Littafin Ya Kunsa 61