IMAMANCI DA NASSI
Wallafar: Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait
Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Ahlul Baiti a Kur’ani da Hadisai :
“Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa”[1].
“Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su”[2] .
Gabatarwar Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait
Lallai yana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukaki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba a cikinsa[3] . Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma.
Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiya ko karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci. Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane, tare da hakan son rai ya rinjayi mutane nan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta. Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku sani ba[4] ”.
Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asali wanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani. Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayan nan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage.
Hakika koyarwarsu ta kare abin da suka bari, kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci. Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawon zamanin da ya gabata.
Hakika majma Ahlul baiti ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalubalen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata. Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta.
Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar gizo-gizo ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa. Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi. Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadannan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yi wa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima. Fatanmu shi ne ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.
Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait
Birnin Kum – Iran
Allah ya halicci mutum bisa dabi’a da daukar mataki da iya daukar nauyi da zai iya kai shi ga halifancin Allah a bayan kasa, ba zai yiwu ga kowane mahaluki ba ya iya wannan al’amari koda kuwa mala’ika ne, domin su an umarce su da su yi sujada gareshi. A wani bangaren kuma mutum yana mallakar wata nau’in dabi’a da takan iya hana daukakarsa da cigaban kamalarsa. Wannan mutum yana dauke da siffofi madaukaka ta wata fuskar, da kuma siffar karkata zuwa ga kaskanci a gefe guda, abin da yake nuna cewa shi abin halitta ne daya da yake mallakar nufi da ‘yanci a kan ya zabi aiki mafi karfi da kuma matakin da ya dace domin gina rayuwarsa. An ba wa mutum wannan ne domin ba shi damar motsawa a dukkan sasanni mafi fadi da yake keta duniyar mariskai zuwa sama da hakan, da kuma nuna cewa samuwarsa tana da wani hadafi da hannun kudura ya zana shi. Ba a halicce shi don wasa ba, ba a kuma bar shi haka nan ba, kamar yadda ambato mai hikima ya fada yayin da ya ce: “Shin kuna tsammanin mun halicce ku don wasa, kuma ku ba masu komowa ne zuwa garemu ba[5] ”.
Kokari a cikin wannan hadafi da tsari da aka shirya su domin kaiwa ga hadafin asasi bai takaita da dan Adam ba, akwai sauran halittu da suke tarayya da shi a wani bangare da nassin Kur’ani mai girma yake cewa: “Ba mu halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu ba muna masu wasa[6] ”. Idan ya tabbata cewa halitta dukkanta tana tafiya da hikima, da tafiyarwar Ubangiji wacce ta hada da mutum, kuma dukkansu masu tafiya ne zuwa ga cimma wani hadifi da ake bukata, kuma cewa kowane abu yana da shiriyarsa, to menene hadafin da saboda shi ne aka halicci mutum? Kur’ani mai girma yana iyakance wannan hadafin da aka halicci mutum saboda shi da fadinsa: “Ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta mini[7] ”. A nan zamu yi la’akari da cewa kalmar taskacewa da togewa (sai don) tana nufin Allah ba shi da wani hadafi da manufa na halittar mutum sai ibada, kalmar don su bauta min tana bayanin sababi da dalilin halitta shi ne, wato mutum halitta ce don ibada ga Allah, Amma tambaya a nan ita ce: Idan hadafin halittar mutum yana takaituwa ne a ibada ba wani abu ba to mecece ibada? Menene kuma hakikaninta? Idan hadafi na karshe na halittar mutum shi ne kusancin Allah da bauta da dan Adam yake samun kamala da ita, to menene yake tunkuda shi domin kaiwa zuwa ga wannan kamalar?
Hakika mutum a dabi’arsa da fidirarsa yana riskar cewa, biyan bukatarsa tana zama ta hanyar da zai iya toshe tawayar da take samunsa, kamar yadda yake riskar bukatarsa ta hanyar abubuwan da sukan iya kai shi ga kamalarsa sai ya motsa domin nemanta, sai dai tambaya a nan ita ce: Ta yaya ne zai kai ga wannan kamalar? Daga nan ne zamu samu hikima ta Ubangiji ta hukumta sanya wa mutum abubuwan da ta hanyar su ne zai iya sani da tarbiyya da rikon hannunsa zuwa ga kamala. Yayin da abubuwan da dan Adam yake riska shi kadai da hankalinsa suka zama sun gajiya a kan su kama hannun shi wannan mutum domin su kai shi zuwa ga tafarkin tsira koda kuwa ya nemi taimakekeniya da dan’uwansa mutum, domin mafi nisan abin da dan Adam yake mallaka shi ne taimakekeniya don fahimtar gaskiya da hakika a iyakar fagen hankali da mariskai, alhalin wadannan fagage biyu ba su isa ba ga riskar hakikanin gaskiya da zata kai ga kamala.
Saboda haka ne hannun gaibi (Taimakon Ubangiji) ya miko domin toshe bukatar mutum wacce take ita ce mafi girman bukatarsa, sai mutum na farko ya zama dan aike daga Allah kuma mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici. Aikin annabawa ga mutane shi ne bayanin ilmi, da kyawawan dabi’u, da sanin gaskiya da zata kai ga kamala da tarbiyya mai kyau, da kuma bayanin ilmi da dan Adam zai iya fahimta, da kuma bukatuwarsa zuwa gareshi, sai dai shi ba ya iya kai wa ga hakikaninsu ta hanyar lalatacciyar tarbiyya, ko kuma mutum yana bukatar lokaci mai tsawo kafin ya kai ga gano su wadannan ilimomi, kamar sunnar Allah ta halakar da dan Adam sakamakon kaucewa gaskiya da kin ta, ko sunnar Allah a kan cewa abin da mutum ya zaba da sannu zai kai shi ga sa’ada da kamala, sai dai shi ne yake barin ta saboda karkatarsa zuwa ga duniya. Sai muhimmancin aiko Annabi ya bayyana a nan domin ya tunatar, ya yi gargadi. Ubangiji mai girma ya ce: “Ka tunatar domin kai mai tunatarwa ne kawai[8]”. Kamar yadda muhimmancin Annabi yake bayyana da wajabcin samar da shi da la’akari da cewa, shi yana misalta jagoranci ne na aiki na gari, domin shi mutum ne cikakke a ayyukansa da dabi’arsa da kuma sadaukarwarsa, wannan shi ne abin da ake cewa da shi muhimmancin tsarkake rai. Mai girma da daukaka yana cewa: “Yana tsarkake su yana sanar da su littafi da hikima”[9].
Idan hadafin halittar mutum ya zama shi ne bauta ga Allah, ga shi kuwa a bisa dabi’arsa an sanya masa damfaruwa da wasilar da zata kai shi zuwa ga kamala, domin shi yana karkata zuwa ga kamala da sonsa na fidira, da muhimmancin annabta domin bayanin hanyoyin wannan shiriya, kuma da bayyana hakikanin gaskiya da takan kai zuwa ga wannan kamalar. Idan haka ne al’amarin yake to menene zai sa bukatar cigaban wannan hadafin da mikuwar wannan sako ya zamanto ta hanyar imamanci da Shi’a suke shardanta nassi a cikinta, da sauran sharudda kamar ilimi na baiwa daga Allah, da kuma isma? Amsa a kan wannan tambaya da waninta na daga tambayoyi yana tilasta mana tambayar kawukanmu kamar haka;
Menenne imamanci a mahangar addinin Allah?
Menene muhimmancinsa?
Bayan mun fita daga mahallin jayayya zai iya yiwuwa mu amsa wannan tambayoyi da suke zowa kwakwalwa game da imamanci da sharuddansa da suka hada da ilmi, da isma, da makamancinsu na daga sharudda na dole a same su ga imami.
Imamanci da halifanci a makarantun Sunna suna da matsayi daya da suka fuskanta da yake bayar da karfi a kan cewa, imami kuma halifa bayan Manzo (S.A.W) yana nufin shugaba, kuma jagora na siyasa da yake tafiyar da sha’anin tsarin musulunci bayan wafatin Manzo (S.A.W). A kan wannan asasin babu wani dalili na sanya jagora ya zama yana dogara da nassi da ayyanawa ta fusakacin Allah da kuma bayanin Manzo, al’amarin an bar shi ne ga al’umma ta zabi wanda ta so ta ga ya cancanta ga tsayuwa da wannan al’amari na jagoranci, domin muhimmancin imami kuma halifa a nazarin wannan koyarwa, ba ya wuce aikin jagorancin siyasa da tafiyar da al’umma ta fuskacin haddodi, kuma yana daga abu na hankali a wannan hanya al’umma ta tsayar da halifa ya zama ta hanyar shawara (shura), ko kuma ta hanyar wakilan al’umma, ko ta hanyar gado. Ya rage mu san menene sharuddan da suka wajaba ga halifa da aka zaba, haka nan zamu iya gani a wannan mahanga ta Ahlussunna suna ganin imamanci da halfanci bayan Manzo jagoranci ne na siyasa shi kenan, saboda haka ya isa ya zama wannan mutumin adali ne ta nahiyar aiki kamar yadda aka sani, kuma ba a shardanta masa ya zama yana da isma da ilimi da Allah ya ba shi ba, ya isa ya zama yana da iko da zai kai shi wannan matsayi a tsarin musulunci. Sakamakon ra’ayinsu game da imamanci da halifanci wani abu ne da bai wuce jagoranci na siyasa ba, kuma haka ya isa ya kasance ta hanyar zabe da shura, da kwace da karfi, da gado, ko wasiyya, kamar yadda yake a bayyane a aikace na ayyuka masu rikitarwa da suka faru bayan wafatin Manzo (S.A.W) da sharadin adalci, da ilimi daidai gwargwado. Saboda haka ne wasu suke tambayar larurar samuwar imami boyayye, ko kuma larurar ya zama ma’asumi, ko larurar ayyana shi da nassi daga manzon Allah (S.A.W).
Amma koyarwar Shi’a tana cewa ne, imamanci da halifanci bayan Manzo (S.A.W) abu ne mai girma na Ubangiji tamkar muhimmancin aiko da Manzo, kuma mai cigaba ce har karshen duniya, sai suka shardanta isma a cikinta hatta kafin balaga, hade da ilimi da yake daga Allah, da kuma nassi na shari’a ga imami. Saboda haka makarantar Sunna ba ta ganin wadannan sharudda da wata ma’ana da kima, kuma ba sa ganin sun dace da aikin da halifa zai yi, sharudda a nan gun mazhabin Ahlul Baiti (A.S) sun wuce na muhimmancin aikin siyasa kawai.
Wannan shi ne mataki na farko, kuma wajan sabani da yake fassara mana sabanin da ake da shi a fahimtar imamanci da kuma kokwanto a mas’alar isma, ko kuma dalili na wajabcin samuwar nassi. Wannan shi ne ya sanya wasu suka yi bincike game asalin nazarin samun nassi domin su kai ga natija zuwa ga cewa; babu wani tarihin da ya nuna hakan a rayuwar imamai. Wannan batun da aka tayar game da imamanci da halifanci da nazarin nassi da kokwanto game da hakan, ya faru ne sakamkon fahimta da Ahlussunna suka yi wa imamanci. Sai dai magana ingantacciya ita ce; imamanci a Kur’ani da Sunna sun wuce wannan fahimta, kuma ta saba gaba daya daga asasinta daga irin wannan fahimta maras zurfi ta ma’anar imamanci da jagorancin al’umma bayan Annabi. Koyarwar Ahlul Baiti (A.S) tana kudurce cewa imamai goma sha biyu suna da muhimmiyar rawar da suka taka da ta lizimta sharudda masu zurfi mafi tsanani daga sharuddan jagoranci na siyasa[10].
Idan aikin imami shi ne makoma na addini, kuma aikinsa a shari’ance yana mikuwa zuwa ga sasanni masu yawa da ya hada da akida, da hukuncin shari’a, da kyawawan dabi’u, da jagoranci, kuma wajibi ne binsa da karba daga gareshi, saboda haka zantuttukan imami ma’asumi da ayyukansa, da abin da ya tabbatar duk hujja ne na shari’a da take hawa kan baligi a wajabci ko uzuri ga wanda bai sani ba daidai da hujjar ayyukan Manzo (S.A.W). Wannan aiki mai girma yana lizimtar abubuwa da yawa kamar haka; Imami ya zama ma’asumi kamar ismar Manzo, da wajabci a kansa na isar da sako kuma da aiki, wannan yana bayyana cewa isma da wannan ma’ana ba sharadi ba ce ga aikin jagoranci na siyasa kawai.
Muhimmancin aikin imamanci ya wajabta kasantuwar imami ya zama masani da dukkan abin da al’umma take bukata zuwa gareshi na rayuwarta da makomarta, kuma dole ya zama mafifici daga duk wanda yake bayan kasa a zamaninsa domin ya samu bayar da hakkin wannan aiki mai nauyi. Shi’a suna da imani cewa Manzo (S.A.W) ba shi da kansa ne ya ayyana halifa ba, sai dai al’amari ne da Allah ya umarce shi da shi, domin hadafin imamanci da kuma al’amarinta ya doru a kan al’amarin cikar sakon annabci da kuma cigaban shiriyar Ubangiji a kan layi daya. Hikimar Allah ta sanya cigaban isar da sakon Allah ya zama ta hanyar ayyana imami ma’asumi ne, imami shi ne wanda ya lamunce samar da maslaha ta tilas ga al’ummar musulmi bayan Manzo (S.A.W).
Ashe kenan matsayin imamanci na akida ba kamar fikihu ba ne na daga hukuncin rassa, wannan shi ne abin da ya sanya imamanci ya zama yana da wadannan sharudda masu fadi masu girma, kuma ya wuce matsayin jagoranci na siyasa kawai. Idan muhimmancin imamanci yana da fadin da ya wuce jagorancin siyasa to dole ne ya zama yana da sharadi da zai tilasta gaskatawa da shi a matsayin wani asasi na addini kai tsaye, saboda abin da yake mai girma na sakon da yake dauke da shi. Shahidus sani a risalarsa: Asasi na hudu shi ne gaskatawa da imamancin imamai sha biyu (A.S), wannan asasi jama’ar imamiyya su na la’akari da shi wajan tabbatar imani, har ma ya zama wani larura daga larurai na mazhabarsu sabanin wasunsu na daga masu saba musu, su sun dauki wannan a matsayin furu’a ne[11].
Saboda haka ne zamu samu cewa, al’amarin ayyana imamai yana wajen hakkin dan Adam ne, kuma ba zai iya zabar wanda yake da isma ba, ko kuma ya gano wanda yake da ilmi na baiwa daga Allah da sauran siffofin da imamai (A.S) suke dauke da su. Rashin kasanewar zabin imamai ta hanyar dan Adam ya yi kama da zabin annabawa da Allah yake zabar wanda ya so, kuma a gane hakan ta hanyar wahayi da nassi. Bambanci tsakanin Annabi da imami shi ne, Allah yana nuna Annabi ta hanyar mu’ujiza da wahayi, imamai kuma ta hanyar mu’ujiza da nassi.
Sharif Murtada yana fadi a risalarsa cikin abin da yake wajibi a kudurce shi game da annabta: Duk sadda Allah madaukaki ya san akwai maslaha a cikin wasu daga ayyukanmu da tausasawarsa, ko kuma akwai fasadi da barna na addini a ciki, kuma hankali ba ya iya gano ta, wajibi ne ya aiko Annabi domin ya sanar da wannan ga mutane, kuma babu wata hanyar gano shi sai da mu’ujiza. Mu’ujiza kuma dole ta kasance ta saba wa al’ada, kuma ta yi daidai da da’awar Manzo din da abin da ya shafi da’awarsa, ta kuma kasance ba za a iya zuwa da ita ba ta bangaren wani mutum, kuma aikin ya zama ya yi daidai da yadda Allah (S.W.T) ya gudanar da shi, idan wannan duk ya faru to wajibi ne a gaskata shi, in ba haka ba to sai rashin gaskata shi ya zamanto ya munana. Daga abin da ya zo a babin abin da ya wajaba a kudurce shi a imamanci da kuma abin da ya biyo bayansa, ya wajabta kasancewar imami ya zama ma’asumi, domin da bai zama hakan ba, da bukatuwa a gareshi ba ta kare ba, wannan kuma yana tukewa zuwa ga samar da shugaba ma’asumi, kuma wajibi ne ya zama mafificin al’umarsa, mafi saninta, saboda munin gabatar da wanda aka fi a kan wanda ya fi shi a hankalce, Idan ya wajaba ya zama ma’asumi to wajibi ne a samu nassi daga Allah a kan hakan, kuma zabar imamanci ta bangaren mutane ya kawu kenan, domin babu wata hanya da mutane zasu iya sanin mai isma[12]. Don haka ne zamu samu nassi da yake daya daga rukunan isma a mahangar Shi’a da yake nuna ajiya ta Ubangiji da take tattare da wannan imami, daga nan ne zamu sami cewa nassi shi ne mai kai wa ga sanin halifa mai bin Manzo (S.A.W) a wannan aiki na addini da ci gabansa.
Idan mahangar musulunci ga halifanci bayan mazo (S.A.W) ta lizimta samuwar nassi da wannan nazari yake gani bayan wucewar Manzo mai tsira da aminci, wanda ya wuce maganar jagoranci na siyasa, ashe kenan menene matsayin musulunci game da shura da wasu mutane suka lizimce ta a matsayin nazari ga shugabancin al’umma maimakon nassi? Kuma menene alakar shura da tabbatar da immanci da ake da nassi game da shi? Zamu bi wannan mas’ala ta fuskacin tarihi da farko, sannan sai mu bujuro da nassi kan halifancin Annabi (S.A.W), bayan haka sai mu yi bincike game da dokokin shura da kuma alakarta da shugabanci da aka yi nassi da shi, domin mu kai ga natija zuwa ga cewa shura ba kawai nazari ne na hukuncin musulunci ba, sai dai wani abu ne na fakewa da shi da ake amfani da shi wajan nuna wadatuwa ga barin shari’ar musulunci, da daukar wata hanya da ta saba mata da take fitar da dokoki da ba su yi daidai da abin da ma’asumi yake a kai ba. Kuma shura ba wani abu ba ne a musulunci sai hanya ce da aka samu domin gyara abin da ya faru na kuskure a tarihin musulunci, da kuma neman ba shi mazauni a cikin shari’ar musulunci, wato ana iya cewa hanya ce ta halatta kuskure da gyara shi, da ba shi mafita da uzuri, ba nazari ba ce da shari’a ta zo da ita ba.
Sanannen abu shi ne musulunci bai bar al’umma haka nan babu fikira game da hukunci ba, domin al’amarin addini da duniya gaba daya ba ya cika sai da samuwar shugaba da zai jagoranci al’umma, yana shiryar da ita, yana jagorantarta ga abin da yake gyara ga rayuwar al’umma da makomarta. Saboda haka suka ce: Musulunci ya bar al’umma ta zaba wa kanta hanyar hukunci da kuma abin da take gani shi ne mafi maslaha ga kiyaye tsarinta da kuma kare shari’a, wannan kuwa ba yana nufin ya bar ta haka nan ba. Saboda haka wani ra’ayi ya bayyana a tarihin musulunci yana mai jingina al’amarin hukunci da jagoranci daidai da abin da ya faru a tarihi a lokacin sahabbai.
Ahlussunna suna ganin wannan mas’ala mai girma addini ya gafala ga barin ta a Kur’ani da Sunna, ya kuma dora nauyin yin hakan a kan al’umma da su zabi yadda suka so. Idan kuwa haka ne, muna iya tambaya cewa: Shin akwai wata ka’ida ayyananniya da al’umma zata iya dogara da ita wajan ayyana halifa? kuma yaya matsayinta yake a shari’a? Amsa: Sai suka ce: Akwai fuska uku ta ayyana halifa:
Ta farko: Zabin shugabannin al’umma da ayyana jagoranta, wannan kuma ana cewa da shi tsarin shura. Sai dai tsarin shura bai dauki salo daya ba gun sahabbai, saboda haka sai suka samu sabani suka ce shura kala biyu ce:
A-Tsarin shura na farko kamar yadda ya faru a bai’ar Abubakar da Ali dan Abi Dalib.
B-Tsarin shura ta hanyar ayyana wasu adadi da halifan da ya rigaya ya yi, kamar yadda Umar ya yi.
Ta biyu: Wasiyya: Ita ce halifa kafin ya mutu ya sanya wanda zai maye gurbinsa, kuma wannan ma ya dauki salo daban-daban har guda uku:
A- Ya sanya halifa daya kamar yadda Abubakar ya yi a lokacinsa ga Umar.
B- Ya sanya wasu jama’a da dayansu zai zama halifa kamar yadda Umar ya yi tsakanin mutane shida da zasu zabi halifa tsakaninsu.
C- Ya sanya halifanci ga mutane biyu ko sama da haka ya kuma sanya ta mai bin juna kamar ya ce: Halifa bayana shi ne wane, idan ya mutu sai wane. A wannan tsari halifanci yana zama a jere kamar yadda ya tsara shi, kamar yadda Sulaiman dan Abdulmalik ya yi ga Umar dan Abdul’Aziz, sannan Yazid dan Abdulmalik bayansa, haka nan Haruna ya sanya ta ga ‘ya’yansa uku.
Ta uku: Sa karfi, da mamaya, da kwace, da galaba da takobi: Ahmad dan Hanbal ya ce: Imamanci na wanda ya yi nasara ne[13].
A zahiri wannan nazarori gaba dayansu neman gyara kurakuran da wannan al’umma ta yi ne, domin wannan ba shi da wata madogara ko mahanga ta shari’a. Kawai wannan domin gyara abin da ya faru ne a tarihi da kuma neman ba shi halacci na shari’a da kuma neman kare kurakuran magabata na farko daga tuhumarsu daga wannan aiki mai hadari da suka gabatar ba tare da wani dalili na shari’a ba, da kuma neman wanke su daga munanan sakamakon abin da wadannan ayyuka na su suka haifar a sakamakon haka. Saboda haka ne ma kallafawa kai bayani da nema musu uzuri ya bayyana a wannan nazari kamar yadda yake a fili, wannan kuma saboda:
1- Kowanne daga wadannan hanyoyi uku babu wani dalili na shari’a da ya dogara da shi gaba daya, hatta da malamai daga sahabbai ba su san shi ba a bisa hakika.
2- Asalin shura da aka fada a fuska ta farko wanda aka samu daga bai’ar da aka yi wa Abubakar bai faru ba a bai’arsa, kuma ba wanda ya taba da’awar hakan, har ma Umar ya ambace ta da cewa ita bai’ar kuskure ce ba tare da shawara ba, Sai dai wadanda suka zo daga baya sun ba da surar shura domin su ba ta sabon tufafi na shari’a a zabar halifa na farko, wasu ma sun so su ba ta siffa na ijma’i[14].
3- Tsoron faruwar fitina ya zama uzuri da aka zaba wajan wanke farkon bai’ar da aka yi ga halifa na farko yayin da wannan ya faru ba tare da shawara ba, ba a kuma saurari manyan sahabbai ba daga Muhajirun da Ansar wadanda ya kamata su tsinkayi wannan uzurin da aka bayar na gaggautawa domin tsoron sabani da fitina ba, wannan kuwa ya bayyana a nassin hadubar Umar.
Sai dai abin mamaki! Sai ga fitina din ta zo ta dawo hanyar shari’a da ake amfani da ita wajan zaban halifa kamar yadda muka yi bayani a hanya ta uku, ta yadda ake ganin hatta da sa karfi da mamaya da rinjaye da takobi hanyoyi ne na kai wa ga halifanci, kuma wanda ya yi galaba shi ne halifa na shari’a kuma wajibi ne a bi, kuma wannan hanya budaddiya ce ga duk wanda yake mai kwadayi. Ashe akwai wata fitina da ta wuce wannan?!
Farra’u a littafin Ahkamus suldaniyya yana cewa: Babu jayayya a kan tabbacin hakkin halifa a kan wasiyya ga wanda zai maye gurbinsa, kuma babu kokwanto a kan zartuwar wannan wasiyya, domin imami shi ne ya fi cacanta ta da ita, zabinsa yana ga abin da ya zartar kuwa wannan ba ya dogara da ma’abota ra’ayi da fada aji na al’umma[15], wannan yana zama na halifa ne saboda tsoron faruwar fitina da kuma rashin zaman lafiyar al’umma[16] saboda haka wasu daga sahabbai suka rika koma wa Umar dan Khaddabi suna tambayarsa ya yi wasiyya ga wanda zai maye gurbinsa[17]. Ibn Hazam ya karfafi wannan ya ce: Mun samu cewa nada jagoranci yana inganta ta wasu fuskoki:
Na farko kuma mafi inganci mafifici shi ne shugaba mai mutuwa ya yi wasiyya zuwa ga wani mutum da yake zaba shugaba bayan mutuwarsa, shin ya yi hakan a lokacin lafiyarsa ko lokacin mutuwarsa ne, kamar yadda Manzo ya yi ga Abubakar, ko kuma Abubakar ya yi ga Umar, ko kuma Sulaiman dan Abdulmalik ga Umar dan Abdul’Aziz. Ya ce: Wannan fuska da muka zaba waninmu ya yi musunta, kuma mun zabe ta ne saboda abin da yake cikinta ne na cigaban saduwar jagoranci ba katsewa, da kuma tsaruwar al’amarin musulunci da ahlinsa, da kuma dauke abin da ake tsoro na sabani da rikici da ake zaton faruwarsa na daga rashin zaman lafiya, da kuma tsoron kada sirri ya yadu kuma kwadayin wasu ya tashi[18], Sai dai nassi da aka yi da’awrsa ga Abubakar daga Manzo bai tabbata ba, domin babu nassi ga Abubakar shi a kan kansa da cewa shi ne shugaba bayan Manzo (S.A.W), kai ba ma wanda ya taba cewa akwai shi, kai al’umma sun hadu a kan ma babu shi, domin duk wanda yake son ya tabbatar da nassi ga Abubakar to dole ya kore al’amarin da ya faru a Sakifa a dunkule da kuma a rarrabe, kuma ya karyata duk abin da ya zo a sihah na maganar Abubakar, da Umar, da Ali, da dan Abbas, da Zubair, game da halifanci. Saboda haka dole ya rusa dukkan abin da a zo na daga nazarin Ahlussunna game da Manzo (S.A.W) da imamanci, wannan nazari ba a gina shi a kan asasi daya, wato bai’a ga Abubakar ta wannan hanya da ta faru a Sakifa da kuma abin da ya biyo baya! Amma daga faruwar wannan abu ne nazarin shura ya samo asali tsakanin manyan al’umma, saboda haka babu wani ijma’i da ya tabbata, ijma’i a kan nassi game da Abubakar korarre ne[19]”. A nan ne Gazali ya kawo wata magana mai daidai da wannan ijma’i yana mai rushe maganar Ibn Hazam, Gazali yana fadi da alamar tambaya cewa: Don me ya sa ba ku ce nassi wajibi ne ya zo daga Annabi ko kuma daga halifa ba domin ku yanke cibiyar sabanin da ake yi? Sannan sai ya amsa da cewa: Da wasiyya ta kasance wajibi da Manzo (S.A.W) ya yi, alhalin bai yi wasiyya ba, Umar ma bai yi ba[20].
Yayin da Ibn Hazam ya ci gaba da kawo nazarinsa sai ga shi yana kore asalin nazarin shura da kuma kore maganar hakkin zabar shugaba ta hannun manyan al’umma, yana mai dogaro da zabar halifa ta hanyar nassi! Saboda ya nutsu da wajabcin nassi, sai dai shi yana nufin nassin da ya yi daidai da abin da ya faru, koda yake babu wani dalili a kan hakan. Hakika nassi bai saba da asalin nazarin shura ba har abada, shura a nan ba al’amari ne da ba shi da abin da ya kebance shi da wani yanayi ba, kuma dattijan al’umma ba su da hakkin su zabi wanda suka so haka nan kawai ba wani dalili, domin shura tana da iyaka, wannan kuma iyakar nassi ne ya zana mata ita. Suka ce: Daga sharadin shugaba ya kasance bakuraishe, imamanci ba zai yiwu ba sai da shi, suna masu kafa dalili da nassi tabbatacce a kan haka, hakika ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Imamai daga Kuraish ne”. A wata ruwaya yana cewa: “Ku gabatar da Kuraish kada ku shiga gabanta” tare da samun wadannan nassosi da kowa ya sallama a kansu babu wata shubuha ta mai jayayya[21], ko zancen mai sabawa da za a yi la’akari da shi. Suka kuma shardanta wa wannan bakuraishe ya zama na ainihi daga kabilar Bani nadar dan Kinanata, domin ya yi daidai da nassi[22].
Ahmad dan Hanbal ya ce: “Ba yadda za a yi wani daga wanin kuraishawa ya zama halifa[23]”. Yana mai kafa dalili da wannan hadisi da tawaturinsa, da kuma fasawar da Ansar suka yi suna masu mika wuya ga muhajirai kuraishawa yayin da suka kafa musu dalili da wannan hadisi a Sakifa[24]. Ibn Khaldon ya ce: Jamhur sun tafi a kan sharadin kuraishanci da kuma ingantuwar halifanci ga bakuraishe koda kuwa ba zai iya daukar nauyin aikin tafiyar da al’amuran musulmi ba[25]. Haka nan nassin shari’a ya tabbatar da tawaturin magana a kan ingancinsa kuma ijma’i a kansa ya tabbata. Abu ne bayyananne cewa wannan ya faru ne yayin da nasara ta tabbata ga nassi a kan asasin shura, yayin da halifa na biyu ya ga wajabcin samuwar nassi a kan wanda zai maye gurbinsa. Sai wannan nassi ya zama ya hade da tsarin siyasa, duk da yana jefar da ka’idar shura gaba daya. Hada da cewa nassin hadisin Annabi mai daraja da daukaka yana cewa: “Shugabanni daga kuraishawa ne” yana mai rushe tunanin shura gaba daya! Sai ya zama wanda ya yi galaba a kan al’umma ya kuma kwace halifanci da takobinsa ya zama bakuraishe halifancinsa ya inganta domin bai fita daga nassin da ya gabata ba. Haka nan ba a la’akari da sharuddan wajibi da suke dole a same su ga halifa kamar ijtihadi, da adalci, da takawa, domin idan halifa ya zama bakuraishe to halifancin sa ya inganta koda kuwa ya zama mai rauni ko azzalumi. Ashe kenan al’amarin shura ya kamata ya zama ya fita daga wajen nassi, kuma ba zai yiwu a zabi wani ba sai bakuraishe na asali.
A takaice wannan mas’ala tana tabbatar mana da samuwar nassi ingantacce a wannan nazari ta wannan hadisi: “Shugabanni daga kuraishi ne” hakika Buhari da Muslim da ma’abota Sunnan da Siyar sun rawaito da lafazi mabanbanta, sai dai wannan nassi yana bukatar abin da zai kebance shi saboda wasu dalilai:
1-Nassin da ya gabata “Shugabanni daga kuraish ne”, shi kadai ba ya iya tabbatar da hadafin da ake nema na tabbatar da shugabanci, wannan ya kasance domin kare addini da al’umma, ta yadda sahabbai da kansu sun fahimci wannan al’amari tun karewar zamanin halifanci na gari. A cikin sahihul Buhari ya zo cewa: Yayin da aka yi jayayya tsakanin Marwan dan Hakam yana Sham, da Abdullahi dan Zubair yana Makka, sai wasu jama’a suka tafi wajen sahabi Abi barzatal aslami suka ce: Ya Aba barza! ba ka ganin abin da mutane suka fada cikinsa? Sai ya ce: Ina neman ladan Allah domin na wayi gari ina mai fushi da kuraishawa, domin wanda yake a Sham wallahi ba yana yaki ba ne sai domin duniya, wanda yake yaki a Makka ba yana yaki ba ne sai domin duniya[26].
2-Akwai wasu nassosi ingantattu da suka kebance hadisin da ya gabata, kamar haka: Hakika Annabi ya tsoratar a kan alfahari da nasaba ta kuraish, ya kuma yi gargadin cewa wannan al’umma zata halaka, kuma al’amarinta zai daidaice. Ya zo a cikin Sahilul Buhari, daga gare shi (S.A.W) ya ce: “Halakar wannan al’umma zata kasance a hannun wasu samari na kuraishawa ne”[27]. Yaya kenan za a iya hada wannan nassosi guda biyu mai cewa: “Shugabanni daga kuraish ne” da kuma “Halakar wannan al’umman zata kasance a hannun wasu samari na kuraishawa ne”. Ba makawa a kebance wannan hadisin da abin da ya zo na hadisai game da kuraishawa, wannan kuma kebancewar iri biyu ce:
A-Ta korewa: Akwai hadisai da suka toge wasu mutane daga kuraishawa kuma suka nisantar da su daga fagen girmamawa.
Ibn Hajar Alhaisami a wani hadisi mai sanadi ingantacce cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Mafi sharrin kabilun larabawa: Banu Umayya, da Banu Hanifa, da Sakif”. Ya ce: A wani hadisi ingantace Hakim ya ce: A bisa sharadin shaihaini daga Abi Barzata ya ce: “Mafi kin jama’a ko mutane a wajan manzon Allah su ne Banu Umayya[28]”. Abin da ya zo game da sukan alayen Hakam baban Marwan yana da yawa kuma mash’huri ne, shin ya inganta shugabancin al’umma ya dogara da mafi sharrin kabilun larabawa wanda sune ma fi kin mutane a wajan manzon Allah (S.A.W)! Idan wadannan suka zama masu hukunci a sarari to dole mu shaida da cewa lallai al’umma ta halaka ta karkace ga barin gaskiya, kuma kamata ya yi al’umma ta dawo zuwa ga bin shiriyar manzon Allah (S.A.W) da nassin da ya kawo daga Allah na wasiyyarsa da Ahlin gidansa (A.S) maimakon ta koma tana neman samar wa abin da ya faru mafita da kuma tawilinsa da nassi.
B-Ta tabbatarwa:
Hadisin da yazo yana mai nuna fifikon kuraishawa da zabi a kan sauran kabilu bai tsaya ga nuna da’irai kuraishawa ba kawai, sai dai ya kebance wannan da cewa wasu jama’a daga cikinsu ake nufi sai ya ce: “Allah ya zabi Kinana daga ‘ya’yan Isma’il, ya zabi Kuraish daga Kinana, ya zabi Bani Hashim daga Kuraish, ya zabe ni daga Bani Hashim”[29]. Wannan fifita wa da daukaka ga Bani Hashim a kan sauran kuraish ne.
Ibn Taimiyya yana mai karin bayani game da wannan hadisi yana mai cewa: “Ya zo a cikin Sunna cewa; Abbas ya kai karar wasu kuraishawa da suke wulakanta shi, sai Manzo (S.A.W) ya ce: Na rantse da wanda raina take ga hannunsa! Ba wanda zai shiga aljanna sai ya so ku don Allah da kuma kusancina”. Idan sun kasance su ne mafifitan halitta to ba makawa ayyukansu su ne mafifita ayyuka, mafificinsu shi ne mafificin kowane mafifici na sauran kabilun kuraishawa da larabawa, har da Bani Isra’il da waninsu[30]. Matsayi a nan ba matsayi ne na fifita wa ba shi ke nan, sai dai abin nufi kuraish imaninta ba ya inganta sai ta so su Bani Hashim so biyu; Saboda Allah da kuma domin kusanci da Manzo (S.A.W).
Shin ya inganta kuraish gaba dayanta ta zama daidai a wajan gabtarwa a shugabanci da imamanci, kuma akwai Banu Hashim da nassi ya daukaka su zuwa mafi daukakar matsayi, da akwai kuma Banu Umayya da nassi ya kaskantar da su zuwa mafi kaskancin martaba?! Idan abin da ya wakana ya kai mu zuwa ga wannan halin, to shi kenan sai mu shaida da cewa abin da ya faru kauce wa daga hanya ta gari ne, ba mu yi kokarin gyara shi ba.
A takaice yana iya bayyana a fili cewa, a nan mu mun yi duba sosai don gane da abin da ya shafi bahasin maudu’in imamanci, sai muka ga cewa dalilin da ya sa aka samu wannan cece-kuce dangane da wadannan sabani da ake ta fama da su shi ne, bin wannan al’amari da ya faru, da kuma kokarin gyara shi da kuma sanya shi doka da madogara na asasi a tsarin siyasa da tafiyar da shugabancin al’umma har ya zama doka. Maganganu masu rusa juna da ake samu a lokuta daban-daban sun bayyana a zahiri a wadannan ra’ayoyi, abin da ya sa suka rasa kimarsu a matsayinsu na nazarin musulunci da zai iya warware daya daga manyan al’amuran musulunci masu girma.
Sai ga magana game da nassi na shari’a ba ta tsaya ga shi nassin ba, ba ta kuma lizimtu da aiwatar da sharuddansa ba da iyakokinsa. Shura kuma an nuna cewa abu ne rusasshe da aikin da halifa da ya gabata ya yi na nassi ga mai bi masa, da kuma ra’ayin shura da ra’ayin kwace da rinjaye da karfi da kuma sa karfin takobi. Amma mahangar tsarin shawarar manyan gari (shura) shi ya fi kowanne daga wadannan mahangai shiga duhu. Wani lokaci sai ta zama hannun mutum daya da zai kafa kansa halifa mutum biyu su bi shi kamar yadda ake daura aure, ko mutum hudu su bi shi, ko kuma su zama shida da halifa da ya rigaya zai ayyana ba tare da al’umma tana so ba, kai har abin ya wuce hakan, kai har malami kamar Ibn Khaldon ya sanya makusantan sarki da na gefensa -komai kuwa rashin takawarsu da iliminsu - a matsayin ma’abota kulla shugabanci da warwarewa wadanda irinsu ne suka sabawa halifa Ma’amun kan sanya halifanci zuwa ga Ali Arrida (A.S) bayansa[31].
Wannan al’amari ya faru a rabi na biyu na halifancin Usman, ta yadda ya zamana an samu shugaban masu bayar da shawara wani ne daga makusantansa na Banu Umayya a kebance, wanda ba su da wani fifiko, da daukaka, da kokari, da rigo na addini, tare da yawan wadanda suke da wadannan dabi’u a wannan lokaci! Sai manyan shura suka zama su ne Abdullahi dan Amir, da Abdullah dan Sa’ad dan Abi Sarh[32], da Sa’id dan Asi, da Mu’awiya dan Abi Sufyan, da Marwan dan Hakam.
Dabari ya rawaito cewa Usman ya aikawa Mu’awiya da Abdullahi dan Sa’ad dan Abi Sarh, da Sa’id dan Asi, da Amru dan Asi, da Abdullahi dan Amir, sai ya tara su domin ya yi shawara kan al’amrinsa, sai ya ce da su: Kowane mutum yana da wazirai da masu ba shi nasiha, kuma ku ne waziraina masu ba ni nasiha kuma aminaina, kuma kuna ganin abin da mutane suka gani na in kawar da gwamnonina, in kuma mayar da dukkan abin da da suke ki zuwa ga abin da suke so, ku yi kokarin dubawa ku ba ni shawara. Yayin da suka ba shi shawara sai ya yi aiki da duk shawararsu; ya kuma mayar da su a kan ayyukansu, ya kuma umarce su da tsanantawa ta fuskacinsu, da kuma korar mutane kan iyakoki[33] da kuma hana su komawa wajan iyalansu, ya kuma yi niyyar hana su albashinsu domin su bi shi su bukace shi[34].
Wannan irin al’amura masu karo da juna mustahili ne a same su a nazari daya, ta yadda zai zama nazari mai dacewa da al’amuran tafiyar da sha’anin al’umma da yake da doka da ake iya fahimta. Kuma daidai gwargwadon kokawanto game da ingancin wannan nazari daidai yadda yake kai wa ga rinjayar da dogaro da ingancin nassin shari’a da ya zo daga Annabi (S.A.W) wajan ayyana halifansa. Wannan ita ce irin natijar da Dr. Ahmad Mahmudu Subhi ya cimma yana mai duba nazarin imamanci yayin da ya ce: “Amma ta nahiyar tunani Ahlussunna ba su kawo wani nazari mai karfi ba game da siyasa da zai iyakance ma’anar bai’a da shura da ma’abota nada shugabanci da warwarewa daga manyan al’umma, balle a samu wani abu mai iya bambance mana tsakanin mahanga da abin da ya faru a aikace a zahiri, ko tsakanin abin da yake na shari’a da kuma abin da ya gudana a tarihi a aikace.
Sai ga nazarin Ahlussunna a siyasa ya bayyana a wannan zamanin karshe bayan daula ta tsayu a kan wanda ya fi karfi ya yi mulki kamar yadda ya zo a mafi yawancin wannan ra’ayoyi sun zo ne domin raddi ga nazarin Shi’a mabiya Ahlul Baiti (A.S), Kuma wasu daga wadannan ra’ayoyi aka sanya su a matsayin dalilai na hukuncin shari’a saboda dogaro da usulubin da halifofi uku na farko suka yi shugabanci. Wannan kuma ci baya da faduwa da rashin makama tsakanin shari’a da kuma abin da ya faru game da halifanci ne, balle kuma ga maganganu masu karo da juna na wadannan ra’ayoyi da abin takaici daga karshe suka sanya su a cikin dokokin fitar da hukuncin shari’a. Ba komai ne hadafinsu na yin haka ba sai samar da wani ra’ayi mai kishiyantar mahangar Ahlul Bait (A.S) na samun tabbatar nassi a game da halifanci[35].
Na uku: Muhimmancin da shari’a ta bayar ga abin da shawara ta zartar da kuma alakarsa da halifancin da yake da nassi. Zamu ga mafi muhimmanci madogarar shari’a da wannan nazari na shura ya dogara da shi ita ce wannan aya mai girma ta: “Ka yi shawara da su kan al’amari”. Wannan aya tana lizimta wa shugaba wajabcin shawara a kan wani ra’aryi gun wadanda suke ganin ana magana da Manzo ne da umartarsa da yin shawara, kuma umarni yana nuna wajabci, wannan kuwa yana nuna wajabcin shawara da musulmi, kuma tunda ba za a iya shawartar dukkan musulmi ba gaba daya to wannan yana nuna shawara da ma’abota ra’ayi da tunani na wannan al’umma ne[36]. Da wannan ma’anar zamu iya tambaya cewa; Shin shawara tana nufin ana neman yin ta a kan kanta, ko kuma ita hanya ce da za a cimma wasu hadafofi da ita? Suka ce: Ba makawa shawara ba a nemanta a kan kanta kuma ba tana zaman kanta ba ne, ita shawara hanya ce ta tabbatar da wasu abubuwan da mafi muhimmancinsu sanin ra’ayin wasu da kuma tunaninsu da tattaunawa, Domin idan tunani ya zo daga mahanga daban-daban aka tara shi waje daya sai ya sami kima mai girma wajan sanin makamar siyasa, da hukunci, da kuma tafiyar da al’amura, da tattalin arziki, da aminci, da yaki, a wannan kasa, wannan kuwa yana tabbata ba tare da ma’asumi ba daga ma’abota shugabanci.
A nan hadafin sanya shawara zai bayyana, sai dai menene matsayin shura a shari’a? Kuma shin natijar da za a samu ta hanyar shawara da ijma’i ra’ayin duka ake bukata ko kuma ra’ayin mafi yawa za a dauka? Kuma shin ya zama dole ga shugaba ya yi riko da wannan ko kuwa?. Malaman Ahlussunna suna bayar da amsa kala biyu ne a kan hakan:
Na farko: Masu ganin sakamakon shawara ya zama dole ne ga shugaba ya yi riko da shi. Daga cikin wadannan akwai Muhammad Abduh da yake fada a bayanin ma’anar Ulul’amri da yake cewa: Ulul’amri su ne masu shugabantar al’umma a hukunci, kuma wannan su ne aka yi nuni da su a fadin Allah madaukaki: “Al’amarinsu shawara ne tsakaninsu” ba kuma zai yiwu ba shawara ta samu tsakanin dukkan al’umma, don haka ya zama dole a samu wasu jam’a masu wakiltar al’umma, da ba kowa ne ba su sai ma’abota girma da daukaka na wannan al’umma da aka yawaita ambatonsu, yana mai karawa da cewa: Wajibi ne a kan shugabanni su yi hukunci da abin da manyan al’umma suka zartar”[37].
Na biyu: Ra’ayin da yake ganin shawara a matsayin fuskantarwa kawai, babu wani kima da take da shi na shari’a a wajan tilasta shugaba ya yi riko da ita wajan zartar da abin aka hadu a kansa, ko kuma abin da mafi yawa suka tafi a kai.
Daga cikin wadannan akwai Kurdabi, yayin da yake cewa a tafsirinsa “Shawara ta ginu ne a kan sabanin ra’ayoyi, mai shawara yana duba wadannan sabani ne, ya kuma duba wanda ya fi kusa da littafi da sunna in zai yiwu, idan Allah ya shiryar da shi zuwa ga abin da ya so sai ya yi niyyar aiki a kansa ya kuma zartar yana mai dogara gareshi”[38].
Amma malaman Shi'a sun tafi a kan ra’ayi na biyu a tafsirin ayar shura, Muhammad Jawad Balagi yana cewa: “Ka shawarce su a kan al’amari” ai ka nemi gyaransu, da kuma karkato zukatansu da shawara, ba wai domin zasu sanar da kai ilimin daidai ba ko sanar da kai ingantaccen ra’ayi ba, yaya kuwa zasu iya hakan alhali Allah (S.W.T) yana cewa: “Ba ya magana ta son rai, shi (al’amarin) ba komai ba ne face dai wahayi ne da aka yi” saboda haka idan ka yi niyya a kan abin da Allah ya umarce ka da hasken annabta ya kuma datar da kai a cikinsa sai ka aikata kana mai “ka dogara ga Allah”[39].
Shura a nazarin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) tana nuna cewa ra’ayin musulmi ba ya lizimtar Annabi (S.A.W) yayin da madaukaki yake cewa: “Idan ka yi niyyar aiwatarwa sai ka dogara ga Allah”. Ashe kenan tsayuwa da aiki yana zama a bisa asasin niyyar Manzo (S.A.W) ba bisa abin da muminai suka yarda ba. Sannan shawararsa (S.A.W) ta kasance domin gane ra’ayin musulmi ne ga yadda za a zartar da hukunce-hukuncen musulunci, ita shawarar ba a matsayin fitar da hukuncin shari’a take ba, hada da cewa Ubangiji madaukaki ya ce: “Bai kamata ba ga mumini ko mimina idan Allah ya hukunta wani al’amari ya zama suna da zabi a al’amarinsu, duk wanda ya saba wa Allah da manzonsa hakika ya bace bata bayyananne”[40],
Ashe kenan rinjayar da shawara yana takaita da wajan da Allah da manzonsa ba su yi wani hukunci ba ne, amma abin da suka yi hukunci a ciki, shawara a nan sabo ce ga Allah da manzonsa da kuma bata bayyananne[41].
Saboda haka shura tana da kima ne idan ta amfana wajan daukar dokokin zartarwa na musulunci a dukkan fagagen rayuwa da makamancinta, kuma ba ta zama dole ga imami ma’asumi ba, domin ita ba ta iya shar’anta hukunci sabanin magana da zance da tabbatarwar ma’sumi, tana kebanta ne da wajan da Allah da manzonsa ba su da hukunci.
Amma ta bangaren tarihi kamar yadda muka ambata shura ba ta zama wani tsari na siyasa na shari’a na hukunci ba, domin an kirkiri ra’ayinta ne domin gyara barna da kuskure na tarihi da kuma sanya wannan a matsayin madogarar asasi ta tarihi a tsarin shugabanci na wannan lokaci, kuma mu sani halifanci ba ya tabbata sai da nassi daga Annabi ga halifan da zai zo bayansa.
Bai’a girmamawa ce ga mutum domin ya zabi makomarsa a cikin kira zuwa ga Allah da jihadi a tafarkinsa ko sha’anin hukunci da siyasa. A bisa dabi’a muslunci ba ya son rayuwar musulmi ta kasance ba tare da nufinsu ba da kuma yardarsu ba. Biyayya a nan ita ce mafi muhimmnaci a cikin zartar da ayyukan isar da sako da kira, da kuma ayyukan kasa, da jihadi, da karfafa wa ga bin imamai ma’asumai ta hanyar bai’a. Amma wannan ba yana nufin biyayya ga imami ma’asumi tana saraya ba ne idan ba a yi masa bai’a ba.
Idan bai’a ta kasance to tana karfafa imami da biyayya gareshi ne bayan an tabbatar da samuwarsa. Shin zai iya yiwuwa garemu mu ce: Bai’a sharadi ce ta inagancin biyayya ga imam, ko kuma sharadi ce ta wajabcin biyayya gareshi ta yadda zai zama idan babu bai’a ba shi da imamanci, ko kuma babu inganci ga binsa? Sai mu ce: Bai’a tana karfafa dankon wajabcin lizimtar wilayarsa da biyayya ga jagoracinsa ne, ba tana kafa ko samar da assassin asalin wilayar ba ne ko kuma ta zama sharadi na inagncin biyayya gareshi, domin biyayya da imamanci ba sun tsayu ba ne a kan bai’a ga wanda wilaya ta tabbata gareshi da nassi. Shi ya sa zamu samu cewa, Manzo (S.A.W) ya yi aiki da bai’a a lokacin rayuwarsa kamar yadda yake a fili a bai’ar Akaba ta farko, da bai’ar Akaba ta biyu, da bai’ar Gadir.
Wannan sura ta bai’a da ta faru ga Manzo (S.A.W) tare da cewa wilaya ta tabbata gareshi tun kafin wannan bai’a din. Bai’ar da musulmi sukan yi masa ko rashin bai’ar su gareshi (S.A.W) a game da amsa kiransa ko jihadi ko shugabanci, ba ya canza hakkin Manzo a kan al’umma na biyayya ga al’amarin kira da jihadi da jagoranci.
Haka nan shugabancin imam Ali (A.S) bayan Manzo (S.A.W) da ya tabbata a Gadir, Bai’ar da musulmi suka yi masa a rannan ba ita ce zata tabbatar masa da shugabanci ba ta fuskacin sharia’a duk da Manzo ne ya umarce su da su yi masa tun yana raye, ita wannan bai’ar ba ta kara kimar wilayarsa ta nahiyar shari’a a kan karfafa wilaya da biyayya, Kuma da dama daga malaman Ahlussunna sun tafi a kan kasancewar jagoranci yana samuwa ne ta hanyar wasiyya. Suka ce: Idan wani halifa ya yi wasiyya zuwa ga wani bayansa to bai’ar sa ta kullu domin yardar al’umma da ita ba a la’akari da ita, dalilin haka shi ne bai’ar Abubakar ga Umar ba ta tsayu a kan yardar sahabbai ba[42]. Wannan kenan, tare da cewa ba mu samu bai’a ba tsakanin Abubakar da Umar, abin da ya faru kawai ya yi wasiyya da halifanci ne kawai ba wani abu ba.
Idan haka ne wanda Annabi ya yi wasiyya gareshi shi ya fi cancanta a bi ba tare da wani dalili ba a kan sabawa hakan, kuma al’amarinsa zartacce ne, kuma da wannan ne halifanci ya tabbata ga Ali bayan Manzo kai tsaye, shin al’umma ta yi masa bai’a a kan biyayya ko ba ta yi ba. Bai’a tana kasancewa ne daga alkawarin biyayya da karbar tafiyar da hukunci da tafiyar da al’amuran al’umma, wannan kuwa ba ya yiwuwa sai da bai’a, kuma Abbas ya halartowa Ali da ita sai ya ki karba sai dai a fili a gaban mutane a masallacin Annabi. Sannan da aka zo yin bai’a a kan hakan ne mutane suka yi masa bai’a, haka nan al’amarin ya kasance game da Imam Hasan (A.S), shi ya sa yayin da sauran imamai da Allah ya zabe su ga jagorancin al’umma ya zama ba a yi musu bai’a ba sai aka kange su gabarin tafiyar da hukuma da al’amuran al’umma, amma kuma wannan ba ya cire musu hakkinsu na imamanci, sha’anin al’amarinsu yana daidai da na annabawa ne da al’ummarsu suka saba musu suka hana su tafiyar da jagoranci da shiryarwa da fuskantarwa, ba tare da wannan ya cire musu matsayinsu da Allah ya ba su ba[43].
Ashe kenan matsayin bai’a a lokacin halartar imami ma’asumi ba komai ba ne sai karfafawa ga wanda jagoranci ya tabbata gareshi ta hanyar nassi. Kamar yadda bai’a ba ta iya samar da wilaya ga mutum da aka yi nassin binsa kamar Manzo ko imami, nassi ga imami yana wajabta binsa da haramcin rashin yi masa bai’a.
Idan muka kula da nazari ta fuskancin tarihi muka kuma lura da matakan da Annabi ya dauka wajan tarbiyyar al’umma da wayar da ita game da al’amarin Ubangiji wanda ya shafi halifanci sai mu samu cewa ya karfafa nazarin nassi a kwakwalenmu ne ba shura ba, kuma ba a samu wani waje da Manzo ya ambaci wayar da al’umma da tarbiyyantar da ita a kan nazarin shura ba tun daga saukar fadin Allah madaukaki “Ka gargadi jama’arka makusanta”. Har zuwa saukar fadinsa madaukaki: “Ya kai wannna Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka, idan ba ka aikata ba to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah yana kare ka daga mutane”.
Hakika ya zo daga dan Abbas daga imam Ali (A.S) cewa ya ce: “Yayin da wannan aya ta sauka; “Ka gargadi jama’arka makusanta” ga manzon Allah (S.A.W) sai ya kira ni ya ce: Ya Ali Allah ya umarce ni da in gargadi jama’ata makusanta, sai na samu kunci na san cewa idan na bayyana wannan al’amari to zan ga abin ki daga garesu, sai na kame gabarinsa sai Jibril ya zo mini, ya ce: Ya Muhammad idan ba ka yi abin da Allah ya umarce ka to zai azabtar da kai, saboda haka ka yi mana abinci sa’i daya, ka kuma sanya karfatar akuya, ka cika mana kwano na nono, sannan ka kira duk Bani Abdulmudallib domin in yi musu magana in isar musu da sakon da aka umarce ni da shi, sai na aikata abin da ya umarce ni da shi, sannan na kira su, a wannan lokaci mutum arba’in ne da daya ko ba daya, a cikinsu akwai ammominsa abu Dalib, da Hamza, da Abbas, da Abu Lahab, Ya ce: Sai manzon Allah (S.A.W) ya yi magana ya ce: Ya Bani Abdulmudallib ni wallahi ban san wani saurayi a larabawa da ya zo wa mutanensa da mafifici daga abin da na zo muku da shi ba, ku sani ni na zo muku da alherin duniya da lahira, kuma hakika Ubangiji ya umarce ni da in kira ku zuwa gareshi, wanene a cikinku zai karfafe ni a kan wannan al’amari a kan ya kasance dan’uwana wasiyyina kuma halifata a cikinku?, Imam Ali ya ce: Sai duk mutanen suka tage gaba daya, sai na ce alhalin ni ne na fi kowa karancin shekaru a cikinsu, ni ne ya Annabin Allah zan zama mai taimakon ka a kansa. Sai ya riki kafadata sannan ya ce: Wannan shi ne dan’uwana kuma wasiyyina halifata a cikinku ku ji ku bi daga gareshi, Ali (A.S) ya ce: Sai mutanen suka tashi suna dariya suna cewa da Abi Dalib, ya umarce ka ka ji daga danka kuma ka bi shi”[1].
Haka nan Manzo Allah (S.A.W) ya fara shirya wa al’umma tun daga farawa da makusantansa yana mai nuna wa al’umma halifancin Ali (A.S) bayansa, yana mai wasiyya a kan dan’uwansa da wasiyya da halifanci da kuma wajabta biyayya gareshi, Annabi ya kasance yana mai bayyyana ma’anar ayoyin Kur’ani da suke sauka a kansa game da hakkin Ali musamman ayoyin da suka shafi halifanci da imamanci.
Zamakhshari a tafsirinsa yana fada game da fadin Allah (S.W.T): “Kawai shugabanku Allah ne da manzonsa da wadanda suka yi imani wadannan da suke tsayar da salla suke bayar da zakka alhalin suna masu ruku’i”[2], Wannan aya ta sauka game da imam Ali (A.S) yayin da wani ya tambaye shi yana mai ruku’u a cikin salla sai ya jefa masa zobensa[3].
Domin kawar da rikitarwa da kuma yanke duk wani tawili game da abin da ake nufi da kalmar wali da kuma nuna ko waye a wannan waje sai Annabi (S.A.W) ya bayyana a wajaje da dama cewa: “Ali daga gareni ne, ni ma daga gareshi nake, kuma shi ne shugaban duk wani mumini bayana”[4].
Saboda karfafa shuganbacin imam Ali (A.S) da kuma matsayinsa mai muhimmanci a wajan bayyana sakon musulunci da kuma cimma hadafofin ta hanyar aiwatar da jagoranci domin aiwatar da hukunce-hukunce, da kuma kare su daga dukkan abin da zai iya karkatar da su da kuma canja su bayan Manzo, sai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ali daga gareni yake ni ma daga Ali nake, kuma ba mai bayar wa daga gareni sai ni ko Ali”[5].
Kuma Manzo (S.A.W) ya karfafa wannan ma’ana a aikace, a bayyane, da rana, a kissar isar da sako a surar bara’a, kuma Ahmad dan Hanbal ya fitar da wannan ruwaya a Masnadinsa daga Abubakar yayin da ya ce: “Annabi ya aika ni da bara’a zuwa mutanen Makka, sai ya tafi kwana uku sannan sai ya ce da Ali: Ka yi maza ka riske shi, sai Abubakar ya mayar da ita gareni na isar da ita, yayin da Abubakar ya zo wajan Manzo (S.A.W) sai ya ce: Ya manzon Allah shin wani abu ne ya faru game da ni?! Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ba komai game da kai sai alheri, sai dai ni an umarce ni da kada wani ya isar da sako daga gareni sai ni ko wani mutum daga gareni[6].
A littafin Kusshaf: Abubakar ya rawaito cewa: Yayin da yake kan hanya domin isar da surar bara’a sai Jibril (A.S) ya sauka ya ce: “Ya Muhammad kada wani ya isar da sakonka sai wani mutum daga gareka, sai ya aika Ali”[7].
Daga karshe Kur’ani ya cika wannan maudu’i mai muhimmanci wanda ya shafi haifar da tunani da tarbiyyantarwa a kan yadda al’amarin shugabanci da halifanci zai kasance bayan Manzo (S.A.W) a karshen abin da ya sauka garshi a ayar tablig sannan da kuma ayar cika addini bayan kissar Gadir mash’huriya ta yadda babu wani uzuri ga mai kawo uzuri, Kissar Gadir kissa ce da dayawa sun rawaito ta da dan sabani kadan a wasu wurare Kamar yadda zai zo: Yayin da Manzo (S.A.W) ya dawo daga hajjin bankwana, sai wahayi ya sauka a kansa yana mai tsananta masa: “Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka idan ba ka aikata ba to ba ka isar da sakonsa ba kuma Allah ne yake kare ka daga mutane”[8], sai ya tsayar da jama’a gun Gadir khum, ya tara mutane a tsakiyar rana, ga zafi mai tsanani, ya yi musu huduba yana mai cewa: “An kusa kira na sai in amsa kuma ni mai bar muku sakalaini ne, daya ya fi daya girma, littafin Allah da zuriyata. a ruwayar Muslim[9] da Ahlin gidana ku duba yadda zaku maye mini a cikinsu, domin su ba zasu rabu ba har sai sun riske ni a tafki”. Sannan sai ya ce: “Hakika Allah shugabana ne kuma ni shugaban duk wani mumini ne”. Sannan sai ya kama hannun Ali ya ce: “Duk wanda nake shugabansa to wannan shugabansa ne[10] ya Ubangiji ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, ka taimaki wanda ya taimake shi[11], ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya”[12].
Kuma hakika saukar wahayi da wannan aya ya biyo bayan faruwar wannan abu mai girma da fadin Allah (S.W.T): “A yau ne na kammala muku addininku na kuma cika ni’imata a gareku na yardar muku da musulunci shi ne addini”[13], Wasu hadisai da aka rawaito daga Manzo suna cewa, bayan saukar wannan aya a wannan rana abar halarta wacce ita ce ranar sha takwas ga watan zil-hajji[14] ranar Gadir sai ya ce: “Allah mai girma! Godiya ta tabbata ga Allah a kan kammala addini da cika ni’ima da yardar Ubangiji da manzancina da kuma shugabancin Ali bayana”[15].
A ruwayar Ahmad: “sai Umar dan khaddabi ya gamu da shi –imam Ali- bayan nan, sai ya ce da shi: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Dalib, ka wayi gari ka maraita shugaban dukkan mumini da mumina”[16]. Ba mu samu wani abu ba a rayuwar Manzo (S.A.W) da yake ambaton wani abu da zai iya tabbatar da cewa Manzo ya nufi tabbatar da al’amarin halifanci bayansa in banda nazarin wasiyya a matsayinta na sakon shari’a, ba a matsayin jagoranci na siyasa ba kawai, shi al’amari ne da yake Ubangiji ne da yake aiwatar da zabar abin da ya so na sakon manzancin Annabi (S.A.W) yayin da Kur’ani ya yi nassi a kan Annabi da cewar, idan bai isar da wannan al’amari na sakon halifanci da shugabanci bayansa ba, da bai isar da komai na sakon da ya dauki shekara ishirin yana wahala a kan isar da shi ba[17].
Shahid Sadar (K.S) ya yi muhawarar wannan mas’alar da ta faru a tarihi da bayanai kamar haka; Tsammanin cewa Manzo (S.A.W) ya riki wata hanya ta barin mutane ba magaji ba halifa, da ma’anar cewa Manzo bai taba tarbiyyantar da mutane a kan al’amarin halifanci ba da jagoranci bayansa, wannan kuwa batacce ne domin ya yi karo da matasyin Annabi wanda yake sane da dukkan makomar sakon da ya zo da shi, sannan ya ci karo da hadisai da suka yi Magana game da muhimmancin al’amarin al’umma bayansa a rayuwarsa da kuma kafin wafatinsa a karshen rayuwarsa[18]. Kamar yaddda shahid Sadar ya soke ra’ayi na biyu wanda yake ganin shura da fadinsa: Abin da aka samu daga Manzo da muhajirai da Ansar ya kore batun shura. Domin da Annabi ya dangana al’amari zuwa ga hannun Muhajirun da Ansar bai taskace shi da Ahlin gidansa (A.S) ba, da wannan al’amari ya zama daga mafi bayyanar al’amura da kuma ya wayar da kan al’mmma a kan tsarin shura da bayaninsa dalla-dalla domin mutane su san yadda tsarinta yake. Da Annabi (S.A.W) ya wayar da su a kan haka, to da kuma an samu bayyanar wannan a cikin hadisansa da suke rawaitowa daga gareshi da take dauke da bayani game da shura. Amma sai ya zama ba mu samu wani wanda yake dauke da wannan tunani ba, sai ya zama al’ummar Muhajirun da Ansar duka mun same su ne jama’a guda biyu mabanbanta.
Na daya: Jama’ar da Ahlul Baiti suke jagoranta mai dauke da tunanin wasiyya da Manzo (S.A.W) ya yi game da halifancinsu.
Na biyu: jama’ar mutanen Sakifa da suke bin halifanci da ya biyo bayan wafatin Manzo (S.A.W).
Kuma a dukkaninsu ba wanda yake dauke da tunanin shura kamar yadda tarihi ya nuna, yayin da Abubakar ya yi wasiyya da halifancin Umar bai nemi shawarar kowa ba sai ya dora shi kan halifanci a kan al’umma ba tare da shawarar musulmi ba, ko shugabanninsu, sai Umar shi ma ya tafi a kan wannan tafarki ya zabi wasu wadanda zasu zabi wani daga cikinsu, ya kasance yana cewa: “Da Salim ya kasance rayayye da ban sanya ta shura ba”, wannan kuwa bayani ne karara daga gareshi da rashin imaninsa da shura[19]. Da Annabi ya dauki matakin ya sanya ta shura a tsakanin mutane da ya sanya wannan a da’awarsa tun farko domin ya sanar da wannan al’umma al’amarin sakon Allah da zai iya ba ta damar fuskantar duk wata matsala ta tunani da fikira da wannan kira zai iya fuskanta, yayin da ake samun karuwar budi da shigowar al’ummu jama’a daban-daban.
Sai ya zama ba mu samu komai ba dangane da wannan, kuma abin da aka sani daga sahabbai sun kasance suna jin nauyin fara tambayar Manzo (S.A.W), kai har ma sun bar rubuta sunnar Manzo (S.A.W) duk da kuwa ita ce madogara ta biyu ta shari’a bayan Kur’ani, tare da cewa rubutawa ita kawai ce hanyar da ta rage domin kiyaye ta. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa ‘ya’yan Muhajirun da Ansar ba su da komai a hannunsu na daga abin da ya shafi ilimi game da mas’aloli masu yawa, sai ga shi hatta da kasar da ake ci yaki halifa ba shi da wani hukumci na shari’a game da ita a hannunsa da ya sani; ko a raba ta tsakanin mayaka? ko ta zama wakafi ga dukkan musulmi? Kai har ma sun yi sabani a kan yawan kabbarorin sallar mamaci, wasu suna cewa Manzo ya yi biyar, wasu suna cewa ya yi hudu ne.
Haka nan ya bayyyana a fili cewa Manzo bai kawo shura ba, sai ya zama ba abin da ya rage sai hanya ta uku wacce take cewa Manzo (S.A.W) ya shirya imam Ali da umarinin Allah ya kuma sanya shi halifansa a kan sako da al’umma bayansa a matsayinsa na mai masaniya da zurfin abin da wannan sako ya kunsa da kuma iko a kan kula da tafiyar sakon da cigabansa bayan Manzo (S.A.W), kamar yadda ya tabbata a tarihi a shekaru talatin da ya yi bayan wafatin Manzo (S.A.W) da furucin masu tarihi. Kuma duk abin da da ya zo na hadisai mutawatirai game da Ahlul Baiti (A.S) ba komai ba ne sai karfafa wa ga wannan hanya ta uku, wato ayyana halifansa da umarnin Allah[20].
Abu ne a fili ga wanda ya karanta tarihi cewa imam Ali shi ne wanda ya bayyanar da hadisai da suke nuna halifancinsa bayan Manzo da sunansa (A.S). Kuma ingancin wannan wani abu ne da ma’abota ilimi na wannan al’umma da suka fitar da son rai daga zukatansu suka tabbatar da shi, kuma sama da malami hamsin daga masu sharhin hadisansa sun yi bayanin haka suka kuma kare wannan kariya mai cike da hujjoji da dalilai da suka bayar da nutsuwa a kan hakan[21]. Ali (A.S) shi ne wanda ya dawo wa kwakwalen mutane batun hadisan halifancinsa ba tare da wata jayayya ba, bayan an hana fadin wadannan hadisai a lokacin halifofi da suka gabace shi, yayin da suka hana fadin hadisan manzon Allah sai wanda ya shafi ibada kawai:
1- Ya tara sahabban manzon Allah lokacin halifancinsa sannan ya yi musu huduba yana mai hada su da Allah cewa waye ya ji Manzo (S.A.W) a Gadir khum yana cewa; “Duk wanda nake shugabansa Ali shugabansa ne”, sai ya tashi ya shaida[22].
2- Ali shi ne ya yada wannan hadisin da ya bujuro da shi ga Abubakar da Umar da Annabi yake cewa akwai wanda a cikinku zai yi yaki a kan tawilin Kur’ani kamar yadda na yi yaki a kan saukarsa wanda Abubakar ya yi burin a ce shi ne, haka ma Umar, amma Manzo ya amsa musu da: cewa ba su ba ne. Sannan daga baya Manzo ya gaya wa mutane cewa Ali ne[23].
Wannan ruwaya duk da waninsa sun rawaito ta amma ruwayarsa tana da wani hususiyya domin ya yi ta ne a huduba a gaban mutane, ba hadisi ba ne da ya gaya wa mutum daya ko wasu jama’a, wannan kuwa yana karfafa karfin hadisi game da hakkinsa da yake da yakini da shi, kuma yake da yakini da cewa sauran sahabbai suna da yakini da hakan ba su manta ba.
3- Kuma ya ambaci da yawa daga wadannan hadisai da suke nuna hakkinsa a ranar shura ko bayanta, sai dai an yi sabani kan dalla-dallar maganar da isnadinsa, duk da a dunkule sun tabbatar da hakkinsa, mafi karancin abin da ya hada su da Allah a kansa shi ne abin da Ibn Abdulbar ya fitar a littafinsa yana mai cewa: Ali ya fada wa wadanda suke cikin shura tare: “Ina hada ku da Allah shin akwai wanda Manzo (S.A.W) ya hada shi ‘yan’uwantaka da shi tsakaninsa da shi yayin da ya sanya ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi in ba ni ba? A bayan wannan hadisi Ibn Abdulbar ya sake rawaito wani daga Ali yana mai cewa: Imam Ali (A.S) ya kasance yana cewa: “Ni bawan Allah ne kuma dan’uwan manzonsa, ba mai fadin haka a bayana sai makaryaci”[24].
An rawaito ta a littafin Kanzul Ummal a wani hadisi mai tsawo daga Abu Dufail ya ce: Ali (A.S) ranar shura yana fadin wannan hadisi…[25]. Wanda abin da shi Ibn Abdulbar ya fitar wani yanki ne daga gareshi, sai dai sanadin Kaznul ummal a kwai jahala[26] a cikinsa, shi ya sa ma aka samu jayayya game da shi, an ce Zafir ya rawaito shi wanda shi mutum ne da ba a san shi ba, wasu kuma sun yi musun sa saboda mataninsa amma ba a la’akari da wannan saboda ya ginu ne a kan fahimta ta cewa an yi bai’a ga Abubakar a kan cewa ijma’i ce ko kusa da hakan wacce ba ta da asasi.
Amma isnadi ya kasance saboda Zafir ne kamar yadda Ibn Abdulbar ya rawaito shi a littafin Isti’ab,[27] Ibn Hajar Askalani ya ce: Zafir ba a tuhumar sa da karya, kuma idan aka same shi a hadisi to hadisinsa yana da kyau[28]. A farkon wannan hadisin, Abu Dufail yana cewa: Na kasance a bakin kofa ranar shura sai aka daga sauti sama, sai na ji Ali (A.S) yana cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar amma na rantse da Allah ni na fi shi cancanta, amma sai na ji na bi domin tsoron kada su koma kafirai wasu suna saran wasu da takobi, sannan sai Umar ya biyo bayansa alhalin na fi shi cancanta kan wannan al’amri, amma sai na ji na bi tsoron kada mutane su koma kafirai wasu suna saran wasu, sannan sai ga ku kuna son ku yi bai’a ga Usman! Ba komai zan ji in bi”, Sannan sai ya ambaci al’amrin shura ya fara bayyana musu falalarsa da fifikonsa da darajojinsa da ya fi su da ita, daya daga cikinsu ita ce wannan bangaren da shi Ibn Abdulbar ya rawaito game da ‘yan’uwantakarsa da Manzo (S.A.W)[29]. Wannan hadisi yana da wani mai karfafarsa da zai zo nan gaba.
4- Daga abin da yake nuna cancantarsa fiye da Abubakar musamman yayin da ya fadi karbar surar bara’a daga Abubakar! Nisa’i ya rawaito da sanadi sahihi daga Ali (A.S) cewa manzon Allah (S.A.W) ya aika shi da bara’a zuwa ga mutanen Makka tare da Abubakar, sannan sai ya sa Ali ya bi shi ya ce da shi: “Ka karbi littafin ka tafi zuwa Makka ya ce: Sai ya cim masa a hanya, sai Abubakar ya koma Madina yana mai bakin ciki, sai ya ce: An saukar da wani abu game da ni ne? Sai Manzo ya ce: A’a, sai dai ni an umarce ni da in isar da wannan ko ni ko wani mutum daga gidana”[30]. A dukkan wannan hadisai akwai raddi ga wanda yake cwa Ali bai ambaci wani abu ba da yake nuna shi ya fi cancanta da halifanci, wannan kenan balle mu shiga Nahajul Balaga.
5- Daga mafi shaharar maganarsa bayan labarin Sakifa ya zo masa da kuma mubaya’ar da mutane suka yi wa Abubakar:
ya ce: Me kuraishawa suka ce?
Suka ce: Sun kafa hujja da cewa su ne bishiyar Manzo.
Sai ya ce; Sun kafa hujja da bishiya amma sun tozarta ‘ya’yan itaciyar[31].
6- Kafa hujja da sakamakon Sakifa a fadinsa:
Idan ka shugabance su sakamakon shura
Yaya haka alhalin masu shawara ba sa nan
Idan kuma ka kafa hujja garesu da kusanci ne
To waninka shi ne ya fi cancanta, ya fi kusanci[32]
7- Hudubar shakshakiyya wacce take da karfafuwa daga malamai[33] daban-daban kuma take da ma’ana da take nuni ga hakan a fili dalla-dalla: “Amma wallahi! Hakika wane ya sanya ta (rigar halifanci) alhalin kuma ya san cewa misalin matsayina game da ita kamar matsayin kan inji ne na nika da dutsensa, kwararar ambaliyar ruwa daga gare ni yake gangarowa kuma tsuntsu ba ya iya kaiwa wajena (duk tashinsa), amma sai na sakaya tufafi na kau da kai[34] na kuma cije na kawar da kai, na zama ina mai kai-kawon ko in tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu…! Sai na ga hakuri a kan wannan ya fi lizimtuwa, sai na yi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kuma shakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa! har sai da na farko ya wuce, sai ya mika ta zuwa ga wane bayansa…
Abin mamaki! Yayin da ya kasance yana neman ya sance ta daga wuyansa[35] a rayuwarsa sai ga shi ya kulla (mika) ta ga wani bayan wafatinsa, ya mamakin tsananin yadda suka yi kashe mu raba na abin da yake cikin hantsarta…![36] Sai na yi hakuri tsawon lokaci, da tsananin jarabawa, har sai da ya wuce shi ma sai ya sanya al’amarin halifanci a hannun wasu jama’a da ya raya cewa (wai) ni daya ne daga cikinsu, Kaicon al’amarin shura!, yaushe ne kokwanton fifikon al’amarina a kan na farkonsu ya faru har da zan zama ana sanya ni tsaran makamantan wadannan!…”[37].
Daga wannan magana ta imam Ali (A.S) zamu sani cewa; ashe kenan Abubakar ya san matsayin imam Ali na halifanci da daukakarsa kamar yadda kan dutsen markade da nika yake da daukaka a kan jikin dutsen ne.
Saoba haka ne yake a fili cewa matsayinsa ba boyayye ba ne sai dai mun ga tarihi yana neman ya farar da wani abu na jayayya domin ya yi daidai da abin da ya faru a tarihi, kamar yadda muka samu wasu suna neman musun maganarsa a game da halifanci, wanda da can sun yi musu ga hadisan Manzo (S.A.W). Amma gaskiya tana nan, sai dai abin takaici da tarihi bai karkata zuwa ga Ali ba! Tarihin da ya riga ya tabbatar da cewa imam Ali bai yi bai’a ga Abubakar sai bayan wata shida, sai ya nemi toshe kunnensa game da wannan jinkiri da imam Ali ya yi!
8- Maganarsa bayan shura, yayin da suka yi wa Usman bai’a yana mai cewa: “Wallahi kun sani ni na fi cancanta fiye da wanina, wallahi zan yi hakuri matukar al’amarin musulmi ya kubuta zalunci ya kasance a kaina ne ni kadai, domin neman ladan Allah da falalarsa, da kuma nisantar abin da yake kuna goggoriyonsa na kawa da adonsa”[38]. Ibn Abil Hadid ya samu wannan kalma cikin karshen abin da Ali ya fada a wannan lokaci a maganar da ya nakalto ta a nan bayan ya kawar da duk wani kokwanto game da ingancinta, sai ya ce: Mu muna ambaton wannan abu da ya zo na ruwayoyi masu yawa na imam Ali da ya hada ma’abota shura da Allah, kuma mutane da dama sun rawaito wannan da yawa, amma abin da ya inganta bai kasance da tsawo ba kamar yadda aka rawaito, sai dai bayan sun yi bai’a ga Usman shi ya ki bai’a ya ce: “Mu muna da hakki da in an ba mu sai mu karba, amma idan aka hana mu shi sai mu hau bayan rakuma komai nisan tafiya”. Sannan sai ya ce da su: “Ina hada ku da Allah shin a cikinku akwai wanda Manzo ya sanya shi dan’uwa tsakaninsa da shi in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: A cikinku akwai wanda Manzo ya ce: Duk wanda nake shugabansa wannan shugabansa ne in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: A cikinku akwai wanda Manzo (S.A.W) ya ce: Kai a wajena kamar matsayin Haruna ne gun Musa, in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: Shin a cikinku akwai wanda aka amincewa ya isar da surar bara’a kuma Manzo ya ce: Kuma ba wanda zai isar daga gare ni sai ni ko wani mutum daga gareni, in ba ni ba?
Suka ce: A’a.
Ya ce: Shin ba ku sani ba cewa sahabban Manzo sun gudu sun bar shi a filin daga[39] ba wanda ya rage tare da shi in ba ni ba, ban taba guduwa ba?
Suka ce: E.
Ya ce: Shin kun sani cewa ni ne farkon musulunta?
Suka ce: E.
Sai ya ce: Waye ya fi kusanci da Manzo?
Suka ce: Kai ne.
Sai Abdurrahman dan Auf ya katse maganarsa ya ce: Ya Ali! mutane ne suka zabi Usman, kada ka dora wa kanka laifi (ka damu kanka).
Sannan sai Abdurrahman ya kalli Abu Dalha Al’ansari[40] ya ce da shi: Ya Aba Dalha da menene Umar ya umarce ka?
Sai ya ce: In kashe duk wanda ya saba wa al’umma!
Sai Abdurrahaman dan Auf ya ce da imam Ali: Ka yi bai’a tun da haka ne, in ba haka ba sai ka zama wanda bai bi tafarkin musulmi ba! Kuma mu zartar da umarnin da aka umarce mu da shi a kanka!!
Sai Ali (A.S) ya ce: “Kun sani ni ne mai wannan hakki ba wani ba, wallahi zan yi hakuri matukar al’amarin musulmi ya tafi daidai zalunci ya zamanto a kaina ne kawai…”[41]. Wannan kuma hadisi jama’a da yawa suka rawaito shi, ba ya cikin raunanansu ko wadanda ake kokwanto.
9- Wani ya taba cewa da imam Ali ya dan Abi Dalib kai ka kasance mai kwadayin wanna shugabanci, sai ya ce: Ku ne kuka fi ni kwadayinsa kuma ku ne mafi nisa, amma ni na fi kusanci, kuma ina neman hakkina ne, ku kuma kuna hana ni, kuna juyar da fuskata daga gareshi, yayin da ya kafa masa hujja a cikin mutane sai ya juya yana dimuwa bai san me zai amsa ba”[42].
Ahlussunna sun ce wanda ya fadi haka shi ne Sa’ad dan Abi Wakkas ranar shura, Shi’a kuma sun tafi a kan Abu ubaida ne bayan Sakifa, kowanne ne gaskiya dai muhimmin abu ne wanda ya shahara da kowa Sunna da Shi’a suke rawaito wa kamar yadda Ibn Abil Hadid wanda yake Sunna kuma Bamu’utazili yake rawaitowa[43].
10- Fadinsa: “Ya Ubangiji! ni ina hada ka da kuraishawa da wanda ya taimaka musu, sun yanke zumuncina sun karanta matsayina, sun hadu a kan kwace mini abin da yake nawa ne, sannan suka ce: Ka karba da gaskiya ko ka bari da gaskiya[44],
11- Fadinsa: “Amma bayan haka… Yayin da Allah ya karbi ran annabinsa (S.A.W) sai muka ce mu ne ahlinsa masu gadonsa zuriyarsa majibinta al’amarinsa ba wani ba, ba mai yi mana jayayya kan shugancin Muhammad, kuma kada wani ya yi kwadayin hakkinmu, sai mutanenmu suka mike suka kwace mana hakkinmu na shugabanci, sai ga shugabancin a hannun waninmu…”.
Wannan duk yana daga hudubobin da imam Ali ya yi a Madina a farkon shugabancinsa a lokacin bai fi watanni da karbar halifanci ba[45].
12- Fadinsa: “Amma kwace mana wannan matsayi wannan wani abu ne da kwadayin mutane ya jawo shi, wasu kuma suka yi bakin ciki kan matsayinmu, alhali hukunci na Allah ne, kuma makoma a ranar kiyama tana nan gareshi”. Ya fadi wannan a jawabin wanda ya tambaye shi: Yaya mutane suka ture ku daga wannan matsayi alhali ku kuka fi cancanta da shi.
Sannan sai imam Ali ya cigaba da magana kan wani abin da ya fi ban mamaki na wannan zamani da kamar Mu’awiya zai zo yana jayayya da shi, yana mai cewa “Zamani ya kai munzalin da yanzu ya ba shi dariya bayan ya sa shi kuka”[46].
Kamar yadda ya bayyana a fili na karfafa wa ga hakkinsa musamman, matsayin Ahlul Baiti (A.S) yana iya bayyana garemu daga wadannan kalmomi da suka zo daga gareshi:
1- Fadinsa: “Haka yake, duniya ba za ta taba zama ba hujjar Allah ba a cikinta, ko zahiri mash’huri ko kuma boyayye, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su bace”[47]. Ibn Abil Hadid malamin sunna ne amma yana cewa: A nan Imam Ali (A.S) ya yi nuni da bin mazhabar Shi’a isna ashariyya ne[48].
2- Fadinsa: “Ba a kwatanta alayen Muhammad da wani daga wannan al’umma su ne asasin addini kuma madogarar yakini… su ne suke da hakkin wilaya da jagoranci, kuma wasiyya da gado nasu ne”[49].
Bayan ambaton hakkin jagoranci, wannan al’amari wani abu ne da imam Ali ya yi bayaninsa a fili ko ya yi nuni[50] da shi, amma sai ga shi irin su Dakta Ammara yana neman ya gafala daga wannan hudubobi na imam Ali (A.S) yana neman nuna rashin samun magana ta karara a kan hakan, Da kuma neman kare kagen da ya yi domin ya nuna kalmar “wasiyyi” da ta zo a hadisud dar, da cewa kage ne na Shi’a da suka sanya kalmar wasiyyi maimakon waziri[51] alhalin hadisin da ya zo daga ruwayar Ahlussunna bai zo da wata kalma ba in banda kalmar wasiyyina[52].
3- Hadisin “shugabanni daga kuraishawa ne, kuma suna cikin Bani Hashim, ba na waninsu ba ne, kuma shugabanci ba ya yiwuwa ga waninsu”[53]. Mun riga a baya mun yi nuni da wasu hadisai da suka nuna duk wani fifiko da cancantar Bani Hashim a kan sauran kuraishawa.
4- Fadinsa (A.S): “Ina zaku ne! Yaya kuke kirkirar karya! ga hujjoji a fili, ga ayoyi karara, ga manarori a kafe, yaya ake dimautar da ku?! Yaya kuka makance alhali a cikinku akwai zuriyar annabinku, su ne jagororin gaskiya, kuma alamomin addini, harsunan gaskiya?! Ku sanya su a matsayi mafi kyau na Kur’ani, ku kuma gangaro zuwa garesu irin gangarowar nan ta mai kishirwa. Ya ku mutane ku rike ta daga cikon annabawa (S.A.W) cewa: Duk wanda ya mutu daga cikinmu ba matacce ba ne, kuma duk wanda ya rididdige a cikinmu ba rididdigagge ba ne”[54]. A cikin wannan akwai abin takaici da imam (A.S) ya yi nuni da shi ga wadanda suka bar Alayen Annabi (A.S) bayan hujja da dalilai masu karfi, bayyanannu da suke wajabta bin su.
5- Fadinsa: “Mu kama ce ta tsatson ma’abota jirgin ruwa, kamar yadda wanda yake cikin can ya tsira haka ma wanda yake cikin wannan zai tsira, azaba ta tabbta ga wanda ya bar mu… kuma ni a cikinku kamar kogo ne na As’habul kahafi, kuma ni kamar kofar hidda ce, da wanda ya shige ta ya tsira wanda ya ki shiga ya halaka, ni hujja ce daga watan zilhijja a hajjin bankwana da fadin Annabi (S.A.W) cewa: “Ni na bar muku abin da idan kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba a bayana har abada; littafin Allah da kuma Ahlin gidana”[55].
6- Hudubarsa (A.S): “Ku duba Ahlin gidan Annabinku, ku lizimti tafarkinsu, ku bi sunnarsu, ba zasu taba fitar da ku daga shiriya ba ba kuma zasu taba dawo da ku cikin bata ba… idan suka yi kasa ku yi kasa idan suka tashi ku tashi… kada ku riga su sai ku bata, kada ku yi jinkirin binsu sai ku halaka”[56].
7- Fadinsa (A.S): “… shin ban yi aiki a cikinku da alkawari mafi girma ba, kuma na bar muku (na yi muku wasiyya da) alkawari mafi karanta”[57]. Alkawari mafi girma shi ne Kur’ani, alkawari mafi karanta su ne Ahlul Baiti (A.S) da su ne imam Ali (A.S) da Fadima (A.S) da imam Hasan (A.S) da imam Husain (A.S).
8- Fadinsa (S.A.W): “Mahadi daga cikinmu yake Ahlul Baiti, Allah zai tayar da shi a dare daya”, Ahmad da Suyudi sun rawaito shi daga Ali (A.S)[58]. Da fadinsa: “Mahadi daga garemu yake ‘ya’yan Fadima”, Suyudi ya karbo shi daga Ali (A.S)[59]. Haka nan wadannan ruwayoyi suka zo game da Mahadi daga hadisai masu yawa, da bayanai a fili, da ishara da siffa, da kuma bayanin tarihi tabbatacce.
A takaice muna iya cewa matakin imam Ali (A.S) da yakininsa na hakkinsa a game da halifanci ya kasance yakini ne wanda yake ya samu daga matsayinsa gun Annabi (S.A.W) da kuma rayuwarsa ta hidima ga musulunci, hakika ya kasance a rayuwar Manzo (S.A.W) yana cewa: Allah madaukaki yana cewa; “Idan ya mutu ko aka kashe shi sai kuka juya a kan dugaduganku[60] (kuka bar tafarkinsa)”, Imam Ali (A.S) yana cewa: “Wallahi ba zamu juya a kan dugaduganmu ba, bayan Allah ya shiryar da mu, wallahi idan ya mutu ko aka kashe shi, sai na yi yaki a kan abin da ya yi yaki a kai har in mutu, wallahi ni ne dan’uwansa kuma waliyyinsa dan amminsa mai gadon iliminsa, wanene ya fi cancanta da shi fiye da ni”[61].
A wani wajen Ali (A.S) yana cewa: “Yayin da ya rasu sai musulmi suka yi jayayya a kan mulkinsa bayansa, wallahi bai taba fado mini ba, ban kuma taba tunanin cewa larabawa zasu kawar da wannan jagoranci a bayansa daga Ahlin gidansa ba! ban taba tsammanin za a kawar da shi daga gareni ba bayansa! sai ga mutane sun yi dafifi ga wane suna yi masa bai’a…”[62]. Ashe kenan yana nufin hakkin da mutane suke nemansa, shi kuma ba ya rigonsu zuwa ga nemansa”[63].
Sun kawo matsalar cewa imam Ali (A.S) ya yi wa halifofi uku bai’a, suka raya cewa wannan bai’ar kuma ba zai yiwu a ce domin maslaha ya yi ta ba, ko domin takiyya, ko tilastawa, domin wannan yana nuna tauye matsayi na imam Ali (A.S). Amsar da zamu bayar ita ce: Game da tilasta shi wannan abu ne a fili, da masu tarihi suka rawaito. Buhari yana cewa: “Ali (A.S) ya ki yin bai’a ga Abubakar tsawon wata shida har sai da Fadima (A.S) ta rasu”[64]. A hadubar imam Ali (A.S) ya fadi dalilin da ya sa ya yi bai’a, a hudubarsa da yake cewa:
A- “Na rantse da Allah ba domin tsoron rarraba ba, kafirci ya dawo, addini ya rushe, da mun kawar da wannan jagoranci, amma sai muka yi hakuri a kan wasu zogi da bakin ciki da yake damun mu”[65].
B- Yana fada a Nahajul Balaga: “Sai na duba, sai ga shi ba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) sai na yi wa mutuwa rowarsu, na kuma runtse idanuna a kan wannan kwantsa, na yi himmar hadiyar bakin ciki, na yi hakuri a kan juriya da kuma hakurin dacin da ya fi na madaci”[66]. Shin zai yiwu a zo da wani bayani wanda ya fi wannan zama karara?! In ba haka ba menene ya sa duk wannan bayan irin wannan kokawa da kai kara? alhalin shi ne mafi sanin mutane da halin da ake ciki da sakamakon abin da ya faru.
Da a ce bai kafa musu hujja ba ya baro janazar Manzo (S.A.W) ya tafi Sakifa ya bar jikin masoyinsa (S.A.W) bai wanke shi ba, ya zo ya dora hannunsa a kan hannunsu ya yi bai’a da ba ma’ana ya zo da irin wannan kafa hujja. Idan ya tabbata ta hanya sahihiya Ali dan Abi Dalib (A.S) cewa ya soki nazarin shura ya kuma shelanta cewa ta saba wa shari’a… ya kuma fadi cewa an tilasta shi ne ya yi bai’a ga halifofi uku to bai’arsa ba ta da wani dalili na shari’a a kan halifancinsu kamar yadda wannan ya tabbata a fili daga maganganunsa.
Sannan ya bayyana cewa shi ne ya fi cancanta da halifanci, shin zai yiwu mu ce cancantarsa ga halifanci tana nufin shi ya fi, da ma’anar cewa duk da shi ne ya fi amma da waninsa zai karbi halifanci da ba komai? ko kuwa tana nufin shi ne kawai ya cancanta da halifanci?
Wannan ra’ayi na farko ba daidai ba ne saboda nassin hadisai da kuma maganganun imam Ali (A.S) yayin da yake cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar alhalin ni ne na cancanci in sanya rigata wannan (wato in yi halifanci) daga garesu”. Wannan yana nufin cancantar da ta kebanta da shi, ba wai yana nufin fifikon cancanta ba ta yadda wani ma yana iya cancanta da ita, domin ba ma’anar ya ce rigarsa ce sannan ya zama ba ya nufin cancanta, domin mai riga shi ne mai ita mai cancanta da ita mai mallakarta.
Sannan ga fadinsa da yake cewa: “…Na zama ina mai kai-kawon ko ina tafi da yankakken (shanyayyen) hannu ko kuma in yi hakuri cikin makahon duhu, da babba yake tsufa a cikinsa yaro kuma yake girma a ciki, mumini yake shan bakar wahala a ciki har sai ya riski Ubangijinsa. Sai na ga hakuri a kan wannan ya fi lizimtuwa, sai nayi hakuri amma a cikin idanu akwai kwantsa, akwai kumashakewa (ala-ka-kai) a cikin makogaro, ina ganin gadona abin kwacewa”[67]. Ma’anarsa sai na samu kaina tsakanin ko in karba da karfin da bai isa ba kamar yadda ya zo a fadarsa (A.S): “Saina duba, sai gaba ni da wasu masu taimaka mini sai Ahlin gidana (A.S) saina yi wa mutuwa rowarsu”. Wato daya sami karfi isasshe da ya yaki ma’abota Sakifa kamar yadda yake a maganarsa da aka sani da yake cewa: “Da nasamu mutum arba’in masuniyya da gaskiya da na kawar da mutunen”.
Wannan mataki na imam Ali (A.S) bayadda za a fassara shi da ma’anar yafi cancanta da ma’anar wanima yana iya rikon jagoranci, wannan afili yake cewa ya yi daidai da ma’ana ceta cancantar kebantaka da shi. Hakanan fadinsa (A.S): “Ko kumain yi hakuri cikin makahon duhu…”. Ma’anarsa abin da ya faru ba kawai kwacen mulki ba ne, sai daiwannan yana zama farkon faruwar canji ne da zai iya kai al’umma gabata, Shi ya sa ya karfafa wa mutane bayan kashe Usman dan Affan yayin da suka zo domin yi masa bai’a: “Ku rabu da ni ku nemi wanina domin tafarki ya bice hujja kuma an yi musun ta”[68], da fadinsa garesu: “Ni inaji muku tsoro ne ku kasance cikin wani yanayi na lokaci, alhalin dacan wadansu al’amura sunfaru sun wuce da kuka karkata zuwa garesu karkatar da kuka zamo ba abin yabo ba ne ku a guna”[69].
Dalilan tarihi a rayuwar Annabi (S.A.W) da Ali a kan cewa Manzo (S.A.W) ya kasance yana yana shiryar da Ali da tarbiyya na daukar sako bayan wucewarsa, yana ba shi ilimi da tunani yana kuma kebewa da shi kowane dare da rana, yana wayar da shi a kan abin da sakon musulunci yake dauke da shi da matsalolin tafarkin har zuwa ranar karshe ta rayuwarsa.
Nisa’i[70] ya rawaito da sanadinsa zuwa ga Abi Ishak, ya ce: An tambayi Kusum dan Abbas cewa, yaya Ali ya zama mai gadon Annabi (S.A.W) banda ku? Sai ya ce: Domin shi ne na farkon haduwa da shi kuma mafi damfaruwa da shi”.
Haka nan ya rawaito[71] daga Ali (A.S) ya ce: “Na kasance idan na tambaya sai a ba ni, idan na yi shiru sai a fara –gaya- mini”.
Abu Na’im ya rawaito a littafin Hilyatul auliya daga dan Abbas ya ce: “Mun kasance muna magana a lokacin Annabi (S.A.W) cewa ya ba wa Ali wasiyya (ilimi) saba’in da bai ba wani shi ba”[72].
Nisa’i ya rawaito daga Ali (A.S) ya ce: “Ina da wani matsayi gun manzon Allah (S.A.W) da babu wani mahaluki da yake da shi, na kasance ina zo masa kowane karshen dare sai in ce: Assalamu alaika ya nabiyyallah, idan ya yi gyaran murya sai in koma zuwa ga Ahlina, in ba haka ba sai in shiga wajansa”[73]. Daga gareshi ya ce: “Ina da shiga guda biyu wajan manzon Allah, daya da dare, daya da rana”[74].
Wannan irin tarbiyyantarwa ga Ali da Manzo (S.A.W) ya yi masa ya yi tasirin da Ali ya zama shi ne madogarar kowa makoma ga warware duk wata matsala da aka kasa warware ta hatta da masu jagoranci a wannan lokaci, amma ba a taba samun wata matsala guda daya ba a tarihin imam Ali da ya koma zuwa ga wani mutum ko daya, yayin da a tarihi akwai mas’aloli da dama da dukkkan halifofi suka koma zuwa gareshi duk da kokarin boye wannan matsayi nasa da aka yi.
Amma tarihi ya riga ya tabbatar mana shelantawar da Annabi (S.A.W) ya yi game da hikimar da yake da ita wajan ba wa Ali tarbiyya da ilimi na musamman wanda suna da yawa da suka faru a lokuta daban-daban, kamar hadisuddar, da hadisin sakalaini, hadisin manzila, da hadisin Gadir, da gomomin hadisai[75].
Idan nazarin samuwar nassi ya tabbata ita ce kawai hanyar shari’a da Annabi (S.A.W) ya tabbatar da ita a rayuwarsa a tarihi. Kuma imam Ali (A.S) ya ki dukkan wani abu da zai zama makoma ga jagoranci bayan Manzo in ba wasiyya ba, sai ya rage mana mu yi bincike game da dalili ta fuskacin shari’a da yake tabbatar da cewa Manzo (S.A.W) ya yi wasiyya da imam Ali (A.S) da halifanci bayansa, kamar yadda shi ma ya yi wasiyya da halifanci da imamai bayansa.
Shi’a suna da akidar cewa imamancin imam Ali da ‘ya’yansa Hasan da Husain da kuma tara daga zuriyar Husain (A.S) duk an samu nassi da ya zo game da hakan daga manzon Allah (S.A.W) wanda kuma kowanne daga cikinsu ya yi wasiyya da mai bi masa, nassosin hadisan sun kasu gida uku ne:
Nau’i na farko: Abin da yake wajabta komawa zuwa ga Ahlul Bait (A.S) ba tare ya fadi sunayensu ba; kamar hadisin sakalaini da hadisin safina wadanda mutawatirai ne daga Shi’a da Sunna.
Nau’i na biu: Abin da yake iyakance adadin halifofin Annabi da cewa sha biyu ne kuma daga kuraishawa daga Bani Hashim suke, Wannan kuwa adadi ba ya dabbakuwa sai a kan imamai na Ahlul Baiti (A.S), sabanin idan an dabbaka shi a kan wasunsu.
Nau’i na uku; Hadisan da suka zo da ambaton sunayensu (A.S) har guda goma sha biyu, ta hanyar Shi’a da Sunna.
Tirmizi ya rawaito daga Jabir yana cewa: “Na ga manzon Allah (S.A.W) a hajjin bankwana yana kan taguwarsa da shi da Ali (A.S) sai na ji shi ya ce: “Ya ku mutane na bar muku abin da idan kun yi riko da su ba zaku taba bata ba, littafin Allah da Ahlin gidana”[76]. Tirmizi ya ce: A wannan babi kawai an karbo wannan hadisi daga Abi Sa’id da Zaidu dan Arkam da Huzaifa dan Asid.
A Sahih Muslim da Masnad Ahmad dan Hanbal da Sunan Darimi da Baihaki da wasunsu kuma lafazi ga na farko yake daga Zaid dan Arkam ya ce: “Manzon Allah ya tsaya yana mai huduba a wani ruwa da ake kira Khum da yake tsakanin Makka da Madina… Sannan ya ce: “Ya ku mutune ku sani ni mutum ne da dan sakon ubangijina ya kusa zuwa sai in amsa masa, na bar muku nauyaya biyu; Na farko littafin Allah da akwai shiriya a cikinsa, ku yi riko da littafin Allah da kuma Ahlin gidana”[77].
A cikin sunan Tirmizi da masnad Ahmad da lafazin Tirmizi: “Na bar muku abin da da idan kuka yi riko da shi ba zaku taba bata ba bayana, daya ya fi daya girma: littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Ahlin gidana, ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki, ku duba ku gani yaya zaku maye mini a cikinsu”[78].
Daga irin hadisai da suka zo akwai hadisin safina, Manzo (S.A.W) yana cewa: “Ku sani misalin Ahlin gidana a cikinku kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau ya tsira wanda kuma ya bar shi ya nutse”[79].
Wasu malamai da dama suna ganin Ahlin gidan Annabi (S.A.W) su ne mutum biyar masu girma da daraja da ya hada da annabin kansa (S.A.W) da kuma Ali da sayyida zahara da Hasan da Husain (A.S). Wannan kuwa ita ce mahangar da yawa daga sahabbai, wadanda suka tafi a kan hakan sun hada da, Abu Sa’idul Khuduri, da Anas dan Malik, da Wasila dan Aska’a, da Ummul muminin Ummu Salama, da A’isha, da Ibn Abi Salama -agolan Annabi- da Sa’ad dan Abi Wakkas, da sauransu.
Ma’abota tafsiri da ruwayar hadisai da dama sun tafi a kan hakan daga cikinsu akwai; Faharur razi a littafin Tafsirul kabir, da Zamakhshari a Kusshaf, da Kurdabi a Aljami’u li ahkamil kur’an, da Shaukani a Fatahul gadir, da Tabari a Jam’ul bayan an tawili ayil kur’an, da Suyudi a Durrul mansur, da Ibn Hajar Al’askalani a littafin Isaba, da Hakim a Mustadrak, da Zahabi a cikin Talkhis, da imam Ahmad dan Hanbal a littafin Masnad. Wannan kuwa shi ne ra’ayi da yafi zama daidai, shi ya sa ma zamu gani a ruwayar Muslim a sahihinsa da sanadinsa zuwa ga Amir dan Sa’ad dan Abi Wakkas, daga babansa ya ce: Mu’awiya dan Abi Sufyan ya umarci Sa’ad da ya tsinewa imam Ali (A.S) ya ce: Me ya hana ka ka zagi Aba turab? -Kinaya ce ta imam Ali- Sai Sa’ad ya ce: Amma matukar ina tuna uku da Manzo ya fada game da shi ba zan taba zaginsa ba, wallahi ya zama ina da daya daga cikinsu ya fi mini jajayen dabbobi”. Na ji Manzo (S.A.W) yana cewa da shi -yayin da ya bar shi a wani yaki- sai Ali ya ce: Ka bar ni tare da mata da yara? Sai Manzo (S.A.W) ya ce da shi: Ba ka yarda ba da cewa matsayinka a wajena kamar matsayin Haruna ne gun musa sai dai babu wani Annabi bayana. Na kuma ji shi (S.A.W) yana fada a ranar Haibar: Zan bayar da wannan tuta ga wani mutum da yake son Allah da manzonsa, Allah da manzonsa suke sonsa, ya ce: Sai duk muka yi burinta, sai ya ce: Ku kira mini Ali, sai aka zo da shi yana ciwon ido sai ya yi tofi a idanunsa sannan ya mika masa tutar da Allah ya bayar da nasara a hannunsa.
Yayin da ayar Mubahala: “Ka ce ku zo mu kira ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku…” ta sauka sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husain ya ce: Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin gidana”[80]. Tirmizi ya rawaito a sahihinsa da sanadinsa daga Amir dan Sa’ad dan Wakkas ya ce: Yayin da wannan aya ta sauka “Mu kira ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku” sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husain sannan ya ce: Ya Allah wadannan su ne Ahlin gidana”[81]. Haka nan Hakim[82] ya rawaito shi a littafin Mustadrak da Baihaki[83] shi ma a littafin sunna.
Mawallafi littafin Kusshaf yana cewa: Babu wani dalili mafi karfi ga falala da daukaka da ya kai wannan ga ma’abota bargo, wadanda su ne Ali da Fadima da Hasan da Husain. Domin su yayin da yayar mubahala[84] ta sauka ya kira su ya rungume Husain ya rike hannun Hasan, Fadima tana bayansa Ali kuma yana bayanta, da wannan ne aka san ma’anar ayar, kuma ‘ya’yan Fadima da zuriyarsu ana kiransu ‘ya’yansa, kuma ana danganta su ga Manzo dangantawa ingantacciya mai amfani a duniya da lahira[85]. Imam Ahmad ya rawaito a babin falala da sanadinsa daga Shaddad Abi Ammar, ya ce: Na shiga wajan Wasila dan Aska’a, a wajansa akwai wasu mutane sai suka rika maganar Ali (A.S) sai suka zage shi ni ma sai na zage shi tare da su, bayan sun tashi sai ya ce da ni: Ba na ba ka labari ba daga abin da na gani daga manzon Allah (S.A.W) ? Sai na ce: Na’am, Sai ya ce: Na zo wajan Fadima (A.S) ina tambayar ta Ali, sai ta ce ya tafi wajan manzon Allah (S.A.W), sai na zauna na saurare shi har sai da manzon Allah ya zo a tare da shi akwai Ali da Hasan da Husain (A.S), kowannensu yana rike da hannunsa, sai ya zaunar da Hasan da Husain kowanne a kan cinyarsa sannan sai ya lulluba masu tufafinsa -ko kuma bargo- sannan ya karanta wannan aya: “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti ya tsarkake ku tsarkakewa”. Sannan sai ya ce: “Ya Ubangiji wadannan su ne Ahlin gidana, Ahlin gidana su suka fi cancanta”[86]. Tabari ya rawaito shi a cikin tafsirinsa[87] da Tirmizi[88] a cikikn sahihinsa, da Suyudi[89] a Durrul mansur, da Haisami a Majma’az zawa’id[90], da Hakim a Mustadrak[91] da Ahmad a Masnad[92].
Hadisin da Manzo (S.A.W) ya fadi adadin imamai a ciki kuma su sha biyu ne; Manzo ya bayar da labarin adadin imamai da zasu zo bayansa da imami kuma halifa bayansa kamar yadda ma’abota sihah (ingantattun littattafai) da ma’abota masanid suka rawaito kamar yadda zai zo:
1-Muslim ya raywaito daga Jabir daga Samura cewa ya ji Annabi (S.A.W) yana cewa: “Addini ba zai gushe ba yana mai tsayuwa har sai alkiyama ta tashi ko kuma an samu halifofi goma sha biyu a gareku dukkaninsu daga Kuraish”. A wata ruwaya sai Annabi ya fadi wata kalma da ban ji ba, sai na tambayi babana: menene manzon Allah ya ce: Sai ya ce: “Dukkaninsu daga Kuraishi suke”[93]. A wata ruwaya ya ce: “Dukkaninsu daga Bani Hashim”[94].
Ahmad da Hakim sun rawaito da lafazin Hakim daga Masruk ya ce: Mun kasance muna zaune a wani dare gun Abdullahi dan Mas’ud yana karanta mana Akur’ani sai wani mutum ya tambaye shi: ya Aba Abdurrahman shin kun tambayi Annabi (S.A.W) halifa nawa ne zai mallaki al’amarin wannan al’umma? Sai Abdullahi ya ce: Tun da na zo Iraki ba wanda ya tambaye ni wannan kafin kai! Sai ya ce: Mun tambaye shi sai ya ce: “Goma sha biyu ne, da adadin zababbun Bani Isra’il”[95].
Malaman makarantar halifofi sun samu dimuwa wajan bayanin abin da ake nufi da goma sha biyu a wannan ruwaya da aka ambata, kuma zantuttukansu suna karo da juna.
Ibnl Arabi ya fada a sharhin sunan Tirmizi: Sai muka kirga bayan Manzo (S.A.W) sai muka samu sarakuna goma sha biyu sai muka samu Abubakar, Umar, Usman, Ali, Hasan, Mu’awiya, Yazid, Mu’awiya dan Yazid, Marwan dan Hakam, Abdulmalik dan Marwan, Walid, Sulaiman, Umar dan Abdul’Aziz, Yazid dan Abdulmalik, Marwan dan Muhammad dan Marwan, Assaffah…
A nan sai ya kirga halifan ishirin da bakwai na Abbasawa zuwa zamaninsa sannan sai ya ce: Idan muka kirga goma sha biyu, adadin ya kare daga Sulaiman amma idan muka kirga su da daukaka to akwai biyar daga halifofi wato halifofi hudu da Umar dan Abdul’Aziz amma ni kam ban gane wani abu ba game da wannan hadisi[96].
Alkali Iyad yana fada game da amsar wani wanda ya ce: adadin da suka yi mulki sun wuce hakan. Da cewa; wannan magana ba ta da hujja, domin Manzo bai ce goma sha biyu ne kawai zasu yi mulki ba, don haka ba abin da zai hana su fi hakan yawa[97].
Shi ma Suyudi yana bayar da amsa game da hakan ya ce: Abin da ake nufi da sha biyu ana nufin halifofi sha biyu a dukkan zamanin musulunci har zuwa ranar alkiyama da zasu yi aiki da gaskiya koda kuwa ba a jere suke ba[98].
A littafin Fathul Bari: Halifofi hudu sun gabata kuma ba makawa da cikon saura kafin alkiyama ta tashi[99]. Ibnul Jauzi ya ce: A kan haka abin nufi da sannan sai bala’i ya faru ita ce fitina da zata faru kafin alkiyama na daga bayyanar Dujal da abin da zai biyo baya[100]. Suyudi ya ce: Daga sha biyu an samu halifofi hudu da Hasan da Mu’awiya da Ibn Zubair da Umar dan Abdul’Aziz wadannan takwas kenan, sannan akwai tsammanin Mahadi na Abbasiyya, domin shi a cikin Abbasawa kamar Umar dan Abdul’Aziz ne a Bani Umayya, saboda adalcin da yake da shi, sai ya zama biyu ne suka rage wanda yake daya daga cikinsu Mahadi ne saboda shi yana daga cikin Ahlul Baiti (A.S)[101].
An ce: Abin da ake nufi da halifa goma sha biyu a muddar izzar musulunci da karfinsa da kuma daidaituwar al’amura da ya hada da duka wanda musulunci ya samu izza a zamaninsa, musulmi suka hadu a kan halifancinsa[102].
Baihaki ya ce: An samu wannan adadi da wannan siffa da aka ambata har zuwa lokacin Walid dan Yazid dan Abdulmalik, sannan sai aka sami fitina mai girma, sannan sai mulkin Abbasawa ya bayyana, kuma su suna da yawa da sun wuce wannan adadi da aka fada[103].
Suka ce: Wadanda aka yi ittifaki a kansu na daga halifofi uku ne sannan sai Ali har lokacin da aka samu al’amarin hakamaini a yakin Siffaini sannan sai Mu’awiya ya yi da’awar mulki.
Sannan sai suka yi ittifaki a kan Mu’awiya yayin sulhunsa da Hasan (A.S), sannan sai dansa Yazid, amma Husain (A.S) bai samu mulki ba saboda an kashe shi, sannan sai bayan mutuwar Yazid suka yi sabani har sai da suka hadu a kan Abdulmalik dan Marwan bayan kashe dan Zubair, sannan sai suka yi ittifaki a kan ‘ya’yansa hudu; Walid, sannan sai Sulaiman, sannan sai Yazid, sannan sai Hisham, sai Umar dan Abdul’Aziz da ya shiga tsakanin Sulaiman da Yazid, na goma sha biyu shi ne Walid dan Yazid dan Abudulmalik da mutane suka yi ittifaki a kan jagorancinsa bayan Hisham da ya yi mulki shekara hudu[104]. Saboda haka halifancin goma sha biyu ya zama ingantacce da ittifakin musulmi a kan su, kuma Manzo ya yi albishir ga msulumi da halifancinsu a kan riko da musulunci zuwa ga mutane.
Ibn Hajar ya ce: Wannan ra’ayi yana daga mafi kyawon ra’ayi. Ibn Kasir ya ce: Abin da Baihaki ya tafi a kai kuma wasu jama’a suka goya masa baya na cewa abin da ake nufi da halifofi goma sha biyu da aka ambata a wannan hadisi su ne masu jerantuwa har zuwa Walid dan Yazid dan Abdulmalik fasiki da magana ta gabata a kansa da ya shahara da fasikanci da miyagun halaye abu ne wanda yake akwai kokwanto a kansa, domin halifofi har zuwa lokacin Walid dan Yazid sun fi haka yawa kuma dalilin da ya kawo cewa halifofi hudu na farko ne sannan sai Hasan bayansu, domin Ali ya yi wasiyya da shi, sannan sai mutanen Iraki suka yi masa bai’a har zuwa sulhunsu da Mu’awiya, sannan sai Yazid dan Mu’awiya, sannan sai Mu’awiya dan Yazid, sannan Marwan dan Hakam sannan dansa Abdulmalik dan Marwan, sai dansa Walid dan Abdulmalik, sai Sulaiman dan Abdulmalik, sannan sai Umar dan Abdul’Aziz, sannan sai Yazid dan Abdulmalik, sannan sai Hisham dan Abdulmalik, wadannan sha biyar kenan, sannan Walid dan Yazid dan Abdulmalik, sannan idan muka yi la’akari da dan Zubair kafin Abdulmalik sun zama goma sha shida, ta kowane hali su goma sha biyu ne kafin Umar dan Abdul’Aziz, wanda Yazid dan Mu’awiya ya shiga cikin sha biyu. Kuma Umar dan Abdul’Aziz ya fita daga cikinsu, wanda al’umma suka yi ittifaki a kan gode masa da yabonsa suka kuma kirga shi cikin halifofi shiryayyu, kuma al’umma ta hadu a kan adalcinsa, kuma lokacin yana daga mafi adalcin zamuna hatta da rawafidawa suna furuci da hakan.
Idan Baihaki ya ce: Mu ba ma la’akari da wanda al’umma ta yi ittifaki a kansa, to dole ne ya cire Ali da dansa Hasan daga cikinsu domin su ma al’umma ba ta yi ittifaki a kansu ba, domin mutanen Sham gaba dayansu ba su yi musu bai’a ba. Ya ce: Wasu kuma sun sanya mu’awiya da dansa Yazid da dan dan’uwansa Mu’awiya dan Yazid, ba tare da sun kayyade lokacin Marwan ba ko kuma dan Zubair, domin al’umma ba ta yi ittifaki a kan daya daga cikinsu ba, saboda haka muna iya cewa wannan kirga na halifofi uku, sannan sai Mu’awiya, sai Yazid, sai Abdulmalik, sai Walid dan Sulaiman sai Umar dan Abdul’Aziz, sai Yazid, sai Hisham wadannan goma kenan, sannan bayansu akwai Walid dan Yazid fasiki, sai ya zama dole ne ga malam Baihaki ya fitar da Ali da dansa Hasan daga ciki, wannan kuwa ya saba wa abin da malaman Sunna da na Shi’a suka tafi a kai[105].
Na daya: Cewa Manzo (S.A.W) yana nuni da wadannan hadisai zuwa ga abin da zai faru bayansa da bayan sahabbansa, kuma hukunci da aka fada a wannan labari yana nuni zuwa ga abin da zai faru bayansu ne, kamar yaddda ya yi nuni da adadin halifofin Bani Umayya, kuma kamar fadinsa na cewa: “Addini ba zai gushe ba…”. Ai shugabanci da halifofi goma sha biyu zasu yi sannan sai ya koma zuwa ga halin da ya fi wannan muni, kuma farkon Bani Umayya shi ne Yazid dan Mu’awiya zuwa Marwanal himar, kuma adadinsu su goma sha uku ne, ba kuma za a sa Usman ko Mu’awiya ko dan Zubair a cikinsu ba saboda su sahabbai ne, idan muka fitar da Marwan dan Hakam daga cikinsu saboda sabanin da aka samu a kan halifancinsa, ko kuma domin shi an rinjaye shi bayan mutane sun yi ittifaki a kan Abdullahi dan Zubair to adadi ya inganta, yayin da aka fitar da mulki daga Bani Umayya sai fitina mai girma ta faru yakoki suka yawaita har sai da daular Bani Abbas ta tabbata hali ya canja daga yanda yake canji bayyananne. Amma Ibn Hajar ya yi raddi a kan wannan dalili[106] a littafin Fatahul bari.
Na biyu: Ibn Jauzi ya nakalto a juzu’in da Abul-Husaini dan Al-munadi ya tattaro a littafin Al-mahadi, yana cewa: Akwai tsammanin cewa wannan zai faru ne bayan Mahadi da zai bayyana karshen zamani, ya ce: Na samu a cikin littafin Daniyal: Idan Mahadi ya mutu bayansa mutane biyar daga ‘ya’yan babban jika zasu yi mulki, sannan sai biyar daga ‘ya’yan jika karami, sannan sai ya yi wasiyya da halifanci ga wani mutum daga ‘ya’yan jika babba, sannan sai dansa ya yi mulki bayansa, sai ya zama an sami mulki goma sha biyu kowanne imami ne mai shiryarwa. Ya ce: A wata ruwaya sai mutum sha biyu su yi mulki, shida daga ‘ya’yan Hasan, biyar daga ‘ya’yan Husain, wani kuma daga waninsu, sannan sai ya mutu sai zamani ya lalace. Ibn Hajar ya yi ta’aliki a kan wannan hadisi ya ce: Wannan ruwaya tana da rauni kwarai ba za a iya dogara da ita ba[107].
Wasu mutane suka ce: Zai iya yiwuwa Manzo (S.A.W) yana bayar da labarin abubuwan mamaki da zasu faru da fitinu har mutane a lokaci guda su rarrabu da sarakuna goma sha biyu, da yana nufin wanin hakan da ya ce goma sha biyu da zasu yi kaza da kaza, saboda haka ba komai yake nufi ba sai su zama a lokaci daya…”[108]. Suka ce: Ya taba faruwa a karni na biyar a Andulus kawai akwai sarakuna shida kowanne yana cewa shi ne sarki, akwai kuma na Misira da na Abbasiyya a Bagdad banda wanda yake da’awar shugabanci a duniyar musulmi na daga Alwiyyawa da Hawarijawa[109].
Ibn Hajar ya ce: “Wannan zance ne na wanda bai san wata hanya da wannan hadisi ya zo ba in banda ruwayar da ta zo daga cikin littafin Sahihul Buhari kawai”[110]. Samuwarsu a lokaci guda tana samar da rarraba ne, ba zai yiwu ya zama shi ne abin da ake nufi ba[111]. Haka nan ba su yi ittifaki ba a kan wani ra’ayi da ya zo na daga bayanan da suka gabata, sai dai sun yi kokarin rufe ido da kawar da kai daga ruwayar da ta zo daga Annabi (S.A.W) da sunayensu domin ta saba da siyasar Hukuma da Dauloli a Koyarwar halifanci a tsawon zamani, Malaman hadisai sun fitar da wannan ruwayoyi a littattafansu da sanadinsu zuwa ga manyan sahabbai daga manzon Allah (S.A.W)[112].
Daga Abi Abdullahi Sadik (A.S) ya ce: Jibril ya sauka wajan Muhammad (S.A.W) sai ya ce: Ya Muhammad! Allah yana yi maka albishir da abin haihuwa da za a haifa daga Fadima (A.S) wanda al’ummarka zata kashe shi bayanka, sai ya ce: Ya Jibril! Aminci ya tabbata ga Ubangijina ba bukata gareni ga abin haihuwa da al’umma ta zata kashe shi bayana, sai Jibril ya hau ya sauka, sannan sai ya sake fada masa hakan. Sai ya ce: Ya Jibril! Aminci ya tabbta ga ubangijina ba ni da bukata ga irin wannan abin haihuwa da al’ummata zata kashe shi. Sai Jibrilu ya hau ya sake sauka ya ce: Ya Muhammad Ubangijinka yana gaishe da kai yana kuma yi maka albishir da cewa zai sanya imamanci da shugabanci da wasiyya a cikin zuriyarsa, sai ya ce: Na yarda. Sannan sai ya aika wa Fadima (A.S) cewa Allah yana yi mini albishir da da da za a haifa daga gareki, da al’ummata zata kashe shi bayana, sai ta aika masa da cewa babu bukata gareni ga wannan da da al’ummarka zata kashe shi bayanka, sai ya aika mata da cewa, Allah ya sanya imamanci da shugabanci da wasiyya a cikin zuriyarsa, sai ta aika zuwa gareshi da cewa na yarda “Babarsa ta dauki cikinsa tilas ta haife shi tilas kuma cikinsa da yaye shi wata talatin ne har sai da ya isa karfinsa ya kai shekara arba’in sai ya ce: Ka sanya mini in gode wa ni’imarka da ka yi mini da ni da iyayena, kuma in aikata aiki na gari da zaka yarda da shi, kuma ka gyara mini a cikin zuriyata”[113]. Ba domin ya ce ka gyara mini a cikin zuriyata ba, da dukkan zuriyarsa sun zama imamai[114]. Shi’a suna imani da cewa kowane imami ya yi wasiyya da imamin da zai zo bayansa[115].
1- Jawini[116] ya rawaito daga Abdullahi dan Abbas ya ce: manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ni ne shugaban annabawa Ali dan Abi Dalib shugaban wasiyyai, kuma wasiyyaina goma sha biyu ne a bayana, na farkonsu shi ne Ali dan Abi Dalib na karshensu Mahadi (A.S)”.
2- Daga dan Abbas ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Halifofina kuma wasiyyaina kuma hujjojin Allah bayana goma sha biyu ne na farkonsu dan’uwana na karshensu dana”. Sai aka ce ya manzon Allah wanene dan’uwanka? Sai ya ce: Ali dan Abi Dalib, Aka ce wanene danka? Ya ce: Mahadi wanda zai cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci, na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya mai albishir da gargadi, da ya kasance bai rage ba daga duniya sai rana daya da Allah ya tsawaita ranar har sai dana Mahadi ya bayyana sai Ruhul-Lahi Isa dan Maryam ya sauka, sai ya yi salla bayansa kuma kasa zata haskaka da hasken Ubangijinta kuma ikonsa zai kai gabas da yamma”.
3- Jawini da sanadinsa ya ce: Na ji manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Ni da Ali da Hasan da Husain da tara daga ‘ya’yan Husain tsarkaka ne ma’asumai”[117].
Allah bai halicci mutum domin wasa ba kawai, ya halicci mutum domin ibada da shiriya ne; Annabta tana dauke da nauyi ne na gargadi da isar da sakon Allah, imamanci kuma yana dauke da shiryar da mutane zuwa ga wannan shiriya da kuma kama hannun mutane domin su bi wannan shiriya da annabawa suka zo da ita a aikace, ba zai yiwu a san annabta ba sai da wahayi da mu’ujiza, kuma ba zai yiwu a san imamanci ba sai da nassi da yake nuna ma’sumi.
Bai’a ga shugaba ma’abocin wilaya ta gaskiya ba ita ce take tabbatar da wajabcin binsa[118] a matsayinsa na imami da Annabi ya yi wasiyya da shi da binsa ba, kamar yadda ba ta iya tabbatar da imamanci da halifancinsa[119]. Amma shura ba ta iya zama maimakon wasiyya kamar yadda hukuncin da shura take zartarwa ba ya zama wajibi a kan imami ya yi aiki da shi. Manzo (S.A.W) ya yi aiki domin karfafa nassi da wasiyya a kwakwalen musulmi ne, sannan tarihi bai taba tabbatar da zuwan wani abu daga gareshi ba sai wasiyya da nassi da suka zo a cikin hadisai. Amma imam Ali aikinsa gaba daya ya tsayu a kan nassi da wasiyya ne da zuka zo a cikin hadisai yayin da zamu ga yana musun duk wani abu da ya saba wa hakan.
Daga karshe mun samu dalili na ruwayoyi daga Shi’a da Sunna da suke tabbatar da halifanci da imamanci ga imamai goma sha biyu da nassin hadisin Annabi (S.A.W) wanda na farkonsu yake shi ne Ali dan Abi Dalib, na karshensu Mahadi (A.S) da wannan ne wannan nazarin mahangar yin wasiyya ga halifan Annabi (s.a.w) wato; imam Ali (a.s) zata zama ita kadai ce hanyar shari’a da take tabbatar da hanyar sahihiyar ibada da shiriya.
Abin Da Littafi Ya Kunsa
IMAMANCI DA NASSI 1
Wallafar: Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait 1
Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id 1
Ahlul Baiti a Kur’ani da Hadisai 2
Gabatarwar Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait 3
Imamanci Da Nassi 5
Mahallin Sabani Tsakanin Mahanga Biyu 7
Alaka Tsakanin Isma Da Nassi 9
Nazarin Nassi Da Shura 11
Na Farko: Ta Fuskacin Tarihi 12
Na Biyu: Nassin Halifanci Ya Zo Daga Manzo 14
Alaka Tsakanin Bai’a Da Nassi 21
Manzon Allah Ya Yi Kokarin Karfafa Lamarin Nassi 23
Abin da Ake Tsammani Da Abin da Ya Faru A Tarihi 26
Nassin Wasiyya A Hadisan Imam Ali Da Ahlul Baiti 28
Game Da Ahlul Baiti (A.S) 32
Game Da Bai’ar Imam Ali (A.S) Ga Halifofi Uku 34
Dalilan Tarihi A kan Ingancin Mahangar Nassi 36
Dalilin Tabbatar Wasiyya Daga Ruwayoyi 37
Amma Abin da Ya Zo A Nau’i Na Farko 38
Amma Abin Da Ya Zo Game Da Nau’i Na Biyu 40
Dimuwar Da Suka Samu Game Da Fassarar Hadisin 41
Ibnul Jauzi ya fitar a littafin Kashful mushkil ta fuska biyu: 43
Abin Da Ya Zo Game Da Nau’i Na Uku 45
Sunayen Imamai Sha Biyu A Ruwayar Ahlussuna 46
Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice 47